Auta MG Boy mawaki ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood, ya shahara Kuma fitacce ne a masana'antar ya iya Wakokin soyayyah sosai. Yayi fice a wata Waka da yayi Mai suna "Baba Ayi mini Aure". Ya fara Wakokin siyasa ne a shekarar 2022.[1]yayi wakoki da dama.

Takaitaccen Tarihin Sa gyara sashe

Cikakken sunan sa shine Abdurrahman muhammad Garba Wanda aka Fi sani da suna Auta mg boy. An haife shi a ranar 1 ga watan Janairu a shekarar 1993 a cikin jihar kaduna a cikin garin birnin Zaria. marubucin mawaki ne na wakokin soyayya .[2]

Karatu gyara sashe

Yayi karatun firamare da sakandiri a garin Kaduna daga baya ya cigaba da waka, daga wakokin saurare har yazo ya fara na kallo.

Waka gyara sashe

jarumin ya fara Waka tun yana karami, yake son Wakokin Hausa. Yayi suna a shekarar 2020 a wakar da yayi Mai suna BABA AYIMINI AURE. Itace wakar data fito dashi tasa yayi suna a duniya. Kadan daga cikin Wakokin sa.

  • Baba ayimin aure
  • kina zuciya ta
  • Daga ke
  • labari
  • Zuciya
  • Wakar shugaba Buhari

Manazarta gyara sashe

  1. https://manuniya.com/2022/12/09/cikakken-tarihin-auta-mg-boy/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.