Atika bint Yazid
Ātika bint Yazid ( Larabci: عاتكة بنت يزيد ) Gimbiyar Banu Umayya ce. Ita ce 'yar Yazid I, kuma matar Abdul-Malik bn Marwan. Wasu suna kiranta da shedar karatun addinin musulunci musamman Hadisi. Ana kuma kiranta da kyauta yayin da tabada duk kuɗinta ga wani matalauci daga cikin dangin Abu Sufyan.
Atika bint Yazid | |
---|---|
Rayuwa | |
Mutuwa | 8 century |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Yazid I |
Abokiyar zama | Abd al-Malik ibn Marwan (en) |
Yara |
view
|
Ahali | Muawiya II (en) , Khalid ibn Yazid (en) da Abd Allah ibn Yazid (en) |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci |
Rayuwarta
gyara sasheAtika diya ce ga khalifan Umayyawa na biyu Yazid. Ita ce kanwar khalifan Umayyawa na uku Mu'awiya II. Kafin Yazid I ya rasu, yasa aka yi wa dansa bay’ah. Mu'awiya na biyu ya gaji mahaifinsa a Damascus a shekara ta 64 bayan hijira (Nuwamba 683 miladiyya), yana ɗan shekara sha bakwai 17 a duniya. Dan uwanta ya rasu a shekara ta 684, kuma surukinta Marwan ne ya gaje shi, yayi mulki na tsawon shekara daya ya rasu a shekara ta 685. Marwan ya kasance mijinta, Abd al-Malik ya gajeshi a matsayin khalifan Umayyawa na biyar. Ita ce babbar matar Abd al-Malik, babban danta shi ne aka zaba magajin khalifanci.
Ta hanyar zuriyarsa, danta Yazid ya kasance dan takara na dabi'a don maye gurbin khalifanci. [1] Wata zuriyar Larabawa mai daraja ta uwa ta kasance tana da nauyin siyasa a wannan lokaci a tarihin khalifanci, [2] kuma Yazid ya yi alfahari da zuriyarsa ta Sufyani, yana ganin ya fi 'yan uwansa Marwanid. [2] An zabeshi ta wurin ƙanin mahaifinsa, Khalifa Sulaiman ( r. 715–717 ) a matsayin na biyu a jerin khalifanci bayan dan uwansu na farko Umar II, wanda ya yi mulki daga shekarar 717 zuwa [1] 720 [1] [3] Zuriyar Yazid II ta haɗa reshen mahaifinsa Marwanid na daular Umayyawa, a kan mulki tun shekara ta 684, da kuma reshen Sufyani na Yazid I da mahaifansu na ƙarshe Mu'awiya I ( r. 661–680 ), wanda ya kafa Khalifancin Umayyawa. [1]
Atika da Abd al-Malik sun haifi 'ya'ya maza; Yazid II, Marwan al-Asghar, Mu'awiya da wata mace, Umm Kulthum. [4] [5] daga aurensu.
Duk da haka, ansan Atika da cewa ta kasance dangi ga khalifofi Umayyawa goma sha biyu daga cikin goma sha hudu [lower-alpha 1] . Hakan yasa ta cire Hijabinta a gabansu. Babu wata mace da aka sani da tana da irin wannan adadin muharramai tsakanin khalifofi.
Ta tsira daga mutuwar jikanta Al Walid II.
Khalifofi masu alaka da ita
gyara sasheKhalifofin da suke da alaka da ita sune:
A'a. | Halifa | Dangantaka |
---|---|---|
1 | Mu'awiya I | Kaka |
2 | Yazid I | Uba |
3 | Mu'awiya II | Dan uwa |
4 | Marwan I | Suruki |
5 | Abdul Malik | Miji |
6 | Al-Walid I | 'Ya'yan maza |
7 | Sulaiman [5] | |
9 | Yazid II [1] | Son |
10 | Hisham | Dan uwa |
11 | Al-Walid II | Jikan |
12 | Yazid III | Jikoki-jikoki |
13 | Ibrahim bin Walid |
Bayanan kula
gyara sasheNassoshi
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Lammens & Blankinship 2002.
- ↑ 2.0 2.1 Wellhausen 1927.
- ↑ Powers 1989.
- ↑ Ahmed 2010.
- ↑ 5.0 5.1 Hinds 1990.