Ateke Tom
Ateke Tom shugaba ne na gargajiya kuma ya kasance shine wanda ya fara riƙe matsayin Amanyanabo a daular 'Okochiri', kuma ya kasance tsohon shugaban 'yan sintiri ne na Nija Delta, haka zalika ya kasance daga cikin sojojin sa-kai na yaren Ijaw dake yankin Nija Delta a Nijeriya. [1]A shekara ta 2007 a lokacin fada tsakanin sojojin sa-kai da hukumar bada tsaro a jihar Patakwal, Ateke Tom ya rubuta takarda zuwa ga gwamna, Celestine Omehia, don sasanci akan dama da gwamnatin ta bada na yafiya ga duk dan tawaye ko sojin sa-kai da ya miqa kanshi.[2]
Ateke Tom | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a |
Matsayi
gyara sasheA ranar 25, ga watan Nuwamban shekarar 2017, an nada Ateke Tom a matsayin Amanyanabo na farko a Okirichi. Taron nadin ya samu halartar Ezenwo Wike, gwamnan jihar Rivers.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-10-04. Retrieved 2021-05-17.
- ↑ https://www.legit.ng/1137318-former-militant-leader-ateke-tom-crowned-king-niger-delta.html