Asibitin Koyarwa na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua, Katsina
Federal Medical Centre, (Katsina) cibiyar lafiya ce ta Gwamnatin Tarayya dake cikin birnin Katsina, jihar Katsina, Najeriya. An san asibitin da sunan FMC da kuma GH kafin mayar da shi Asibitin Koyarwa na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua. Babban daraktan lafiya na yanzu shi ne Abdullahi Shugaba.[1][2]
Asibitin Koyarwa na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua, Katsina | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina |
Birni | Jahar Katsina |
Coordinates | 12°59′17″N 7°34′36″E / 12.98814669°N 7.57680262°E |
|
Tarihi
gyara sasheAn kafa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya Katsina a tsakiyar shekarun 70s. Asibitin da ake kira General Hospital, Katsina.[3]
CMD
gyara sasheBabban daraktan lafiya na yanzu shi ne (Abdullahi Shugaba).[4]
Asibitin koyarwa
gyara sasheGwamnatin Tarayya ta amince da ɗaga darajar Cibiyar Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Jihar Katsina zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua. Amincewar ya biyo bayan wata yarjejeniyar tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da Gwamnatin Tarayya suka sa wa hannu ranar Talata.[5]
Shugaban asibitin Muhammad ya ce an kai ruwa rana kafin a cimma matsaya wadda zata bada damar a mayar da Asibitin kwararrun zuwa asibitin koyarwa wanda dalibai masu karantar ilimin likitanci daga Jami'ar Umar Musa za su riƙa amfani da wani ɓangare na asibitin wurin karatunsu.[6]
Gudummawa
gyara sasheWaɗanda suka bada gudunmawa wurin cimma wannan ƙudiri sun haɗa da;
- Farfesa Ibrahim Gambari shugaban ma'aikata na gidan gwamnati.
- Ƙungiyar dattijai na Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ahmadu Kurfi,
- Maraɗin Katsina.
- Hukumar lafiya ƙarƙashin jagorancin Dr. Osagie.
- Ma'aikatan gudanarwa na asibitin koyarwa na Katsina ƙarƙashin jagorancin Hajiya Hannatu Aƙilu; Yar majalisar dattijai ta Jihar Katsina.
- Mai girma Sarkin Katsina, HRH Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
- Mai girma Sarkin Daura, HRH Alhaji Faruk Umar Faruk.[7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "FMC Katsina offers services amid resident doctors' strike". Punch Newspapers (in Turanci). 2021-08-02. Retrieved 2022-06-21.
- ↑ "FG Converts Federal Medical Centre Katsina To Teaching Hospital". Channels Television. Retrieved 2022-06-21.
- ↑ "Take-over of FMC by Katsina varsity for teaching hospital 75% done The Nation Newspaper" (in Turanci). 2021-10-24. Retrieved 2022-06-21.
- ↑ "FG Converts Federal Medical Centre Katsina To Teaching Hospital". Channels Television. Retrieved 2022-06-21.
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/fmc-katsina-za-ta-koma-asibitin-koyarwan-jamiar-umaru-musa
- ↑ https://dailytrust.com/katsina-fmc-now-federal-teaching-hospital
- ↑ https://www.channelstv.com/2022/06/02/fg-converts-katsina-federal-medical-centre-to-teaching-hospital/