Asibitin Kelsey Harrison, Asibiti ne mallakar Jiha a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas. Tun da farko ana kiransa New Niger Hospital kuma haka ake kiransa har zuwa shekarar 2009 lokacin da aka gyara shi aka kuma sanya masa sunan Farfesa, Kelsey Harrison, mashahurin farfesa a fannin mata masu ciki da mata a duniya. An buɗe wurin a hukumance ga jama'a a cikin watan Janairun, 2013.[1]

Asibitin Kelsey Harrison
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar rivers
Coordinates 4°47′N 6°59′E / 4.79°N 6.99°E / 4.79; 6.99
Map
History and use
Opening2013
Contact
Address 11 Emenike Street, Diobu, Port Harcourt
Waya tel:07036598133

Hedikwatar asibitin na a Emenike Street, Diobu, Asibitin Kelsey Harrison na bayar da ayyukan; kiwon lafiya, na haihuwa, haɗari da gaggawa, likitan yara, hoto na bincike, kulawar jarirai da kuma ayyukan tiyata na yau da kullun ga masu amfani da shi.[2] A halin yanzu, asibitin na da gadaje kusan 150 na marasa lafiya kuma Cibiyar Kula da Lafiya ta Duniya (ITCC) ce ke kula da shi.[3][4]

A ranar 7 ga Maris 2013, Asibitin Kelsey Harrison ya yi nasarar wajen haihuwar jaririya a karon farko tun lokacin da aka yi wani babban aikin inganta asibitin. Yarinya ce mai nauyin kilogiram 3.4 mai suna Judith Obilor.[5]

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin asibitocin Fatakwal

Manazarta

gyara sashe
  1. "Nigeria Rivers State: Reform and Resource and Governance". Africanexecutive.com. Inter Region Economic Network. 2013-08-31. Archived from the original on 2015-09-12. Retrieved 2014-06-24.
  2. Nengia, Kevin (2013-01-07). "Kelsey Harrison Hospital Begins Operations, Today". The Tide. Port Harcourt, Nigeria: Rivers State Newspaper Corporation. Retrieved 2014-06-11.
  3. "Hospitals". Archived from the original on 19 July 2014. Retrieved 3 August 2014.
  4. Iruoma, Blessing (2013-01-07). "Rivers: Ultra Modern Kelsey Harrison Hospital To Commence Operation On Monday 7". ScanNews Nigeria. Retrieved 2014-06-24.
  5. "Kelsey Harrison Hospital Records First Delivery". Thenewswriterng.com. Writers House Printing and Publishing Company. 2013-03-14. Retrieved 2014-06-24.