Anton Ernst haifaffen Afirka ta Kudu mai shirya fina-finai ne wanda ya shirya fina-finai da yawa a Afirka ta Kudu da ma Turai gami da Arewacin Amurka.

anton ernst
anton ernst
Anton Ernst a gefe

A shekarar 2012, an zaɓi fim ɗinsa Little One a matsayin daga Afirka ta Kudu don samun damar shiga waje yin takarar lambar yabo ta Academy. Fim ɗin ya kuma lashe lambar yabo ta New York International Film Festival a matsayin mafi kyawun fim, inda ya doke wasu fiye da fina-finai ɗari biyu.[1]

Ya shahara da aikinsa a sinimar Afirka ta Kudu kuma ya shirya fina-finan Afirkaans kamar su Jakhalsdans, Stilte, Ek Lief Jou da Number 10.

A shekarar 2014, ya samar da fim ɗin Momentum wanda taurarin shirin sun haɗa da Olga Kurylenko, James Purefoy da kuma Morgan Freeman wanda Stephen Campanelli ya jagoranta kuma Adam Marcus da Debra Sullivan suka rubuta.

Anton Ernst

An shirya shi don jagorantar shirin Finding Jack tare da Tati Golykh kuma duo za su saki fim ɗin da nasu Fina-finan Magic City.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "2013 Winners" (in Turanci). 2013-06-30. Archived from the original on 2021-12-02. Retrieved 2018-09-06.
  2. Ritman, Alex (November 5, 2019). "James Dean Reborn in CGI for Vietnam War Action-Drama". The Hollywood Reporter. Retrieved November 5, 2019.