Anatoliy Kokush ( Ukraine ; an haife shi a shekara ta 1951, Kerch, RSFSR ) injiniyan fina-finai ne na kasar Ukraine, ɗan kasuwa, kuma mai ƙirƙira. A shekara ta 2005, an ba shi lambobin yabo na Oscars guda biyu. Kyaututtukan sun kasance dangane da nau'in lambar yabo ta Kimiyya da Injiniyanci : an ba da guda ɗaya "don kirkir da haɓaka marikar na kyamarar Arm gyro-stabilized na Rasha da kuma Kan Jirgi"; an kuma bashi ɗayan lambar yabon ne "don kirkira da haɓaka jerin cranes na hotuna masu motsi na Cascade". [1] Uwargidan shugaban kasar Ukraine Kateryna Yushchenko ita ta jinjina wa Kokush saboda gudunmawar da ya bayar ga sinimar Yukren da ma duniya baki daya. [2]

Anatoliy Kokush
Rayuwa
Haihuwa Kerch (en) Fassara, 1951 (72/73 shekaru)
Sana'a
Sana'a injiniya
IMDb nm4624648

Kokush ya kammala karatunsa daga Cibiyar Injiniyanci ta Leningrad a 1974. Daga nan ya fara aiki da Dovzhenko Film Studios a Kyiv.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. Academy Awards 2006 – IMDb
  2. Oscar-winning cinematographer revolutionizes film industry Article from Kyiv Post
  3. "The International Kyiv Film Festival nominee page 2007 Archived 26 July 2013 at the Wayback Machine (in Ukraine)

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe