Amici del Mondo World Friends Onlus.
Amici del Mondo World Friends Onlus, kungiya ce mai zaman kanta ta kasar Italiya, mai amfani da zamantakewa [1] don hadin gwiwar kasa da kasa.World Friends kungiya ce da ba ta gwamnati ba, wacce Ma'aikatar Harkokin Waje ta Italiya ta amince da ita ta hanyar Dokar No. 125 ta shekarar 2014, da aka sabunta zuwa Yuli 16, 2016, an yi rajista a cikin rajistar ONLUS da Registry of Legal Persons D.P.R. 361. Gwamnatin kasar Kenya ta amince da ita a matsayin Kungiyar da ba ta gwamnati ba (NGO), a cikin shekarar dubu biyu da sha daya 2011, ta sami wannan takardar shaidar a Ma'aikatar Harkokin Waje ta Italiya.[2] An kafa ta a shekara ta 2001, ƙungiyar tana da ofisoshin ta a Roma kuma tana da ofishin yanki na sa kai a Piedmont, Liguria, Lombardy, Friuli-Venezia Giulia, Veneto, Emilia-Romagna, Lazio, Sicily. Ofishin kungiyar na Africa yana zaune ne a Nairobi.
Amici del Mondo World Friends Onlus. | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2001 |
world-friends.org… |
Manazarta
gyara sashe- ↑ According to Italian Ministerial Decree 266/2003, is inscribed on the ONLUS Registry since 12 February 2004.
- ↑ Acknowledgment obtained on 16 December 2004.