Ambaliyar Tanzaniya ta 2015
Ambaliyar Tanzaniya ta 2015, ta faru ne a ranar 4 ga watan Maris ɗin 2015[1] a yankin Shinyanga, Tanzaniya . Ambaliyar ta faru ne a lokacin damina na Tanzaniya, watannin Maris, Afrilu, da Mayu, inda ruwan sama ya kai kimanin 150mm zuwa 250 mm. [2] Galibin mutane sun kasa tsira daga ambaliyar . A sanadiyar haka mutane a ƙalla 50 ne suka mutu sannan wasu 82 kuma suka samu raunuka. Bayan ƙididdigar asali na mutane 38 da suka jikkata, wasu sun mutu, waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a asibitoci. [3] Ambaliyar ta ƙara shafar mutane kimanin 3,500. [4][5] Gidaje da dama sun lalace saboda ƙanƙara da iska mai ƙarfi. Hakan ya toshe hanyoyi tare da sanya ayyukan ceto cikin wahala. Filin noma mai nisan kilomita 1000 daga Dar es Salaam, birni mafi girma da kasuwanci a Tanzaniya shi ma abin ya shafa, abin da ya lalata talakawa masu dogaro da noma na yankin. Ambaliyar ta yi ɓarna kamar masara da auduga da dabbobi. [1] [5]
Ambaliyar Tanzaniya ta 2015 | |
---|---|
ambaliya | |
Bayanai | |
Ƙasa | Tanzaniya |
Kwanan wata | 4 ga Maris, 2015 |
Duba kuma
gyara sashe- 2015 Ambaliyar Malawi
- Geography na Tanzaniya
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Tanzania floods kill at least 38, damage roads". Reuters.com. 4 March 2015. Retrieved 1 February 2019.
- ↑ "Weather and climate of Tanzania". Expertafrica.com. Retrieved 2016-03-01.
- ↑ "Death toll in Tanzania flooding hits 50". ReliefWeb.int (in English). Retrieved 2016-03-01.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Flood killed at least 38 people in Tanzania". Reuters Africa. March 5, 2015. Archived from the original on January 7, 2016. Retrieved March 5, 2015.
- ↑ 5.0 5.1 "38 people die in Tanzania flood". BBC News. March 5, 2015. Retrieved March 5, 2015.