Amaramudnooru
Amaramudnooru ko Amaramudnur (Village ID 617765) ƙaramin ƙauye ne a cikin Sullia taluk, gundumar Dakshina Kannada, Indiya. Bisa ga ƙidayar 2011 tana da yawan jama'a 4052 da ke zaune a cikin gidaje 895.[1]
Amaramudnooru | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƙasa | Indiya | |||
Jihar Indiya | Karnataka | |||
Division of Karnataka (en) | Mysuru division (en) | |||
District of India (en) | Dakshina Kannada district (en) | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC+05:30 (en)
|
Wannan ƙauyen ya ƙunshi wurare kamar Kukkujadka, Doddathota, Pailar. Wannan ƙauyen yana haɗe da titin Jalsooru Subramanya ta Doddathota da titin Paichar Bengamale zuwa Kukkujadka.
Ƙauyen yana da rassa biyu na Bankin Vijaya suna aiki a Doddathota da Kukkujadka. Wani karamin ofishin gidan waya yana Doddathota sai kuma musayar waya daya da ofishin kungiyoyin JTO yana Doddathota.
Kauyen na kewaye da koren daji. Mutanen nan suna noma canut,[1] kwakwa, roba da koko. Hedkwatarsa tana Kukkujadka.
Ƙauyen yana da cibiyoyin ilimi da yawa waɗanda suka haɗa da Chokkadi High School, GUPS Doddathota, GPS Pailar da Kukkujadka.