Amakula International Film Festival
Bikin fina-finai na Amakula na ƙasa da ƙasa bikin fina-finai ne na shekara-shekara da ke gudana a Uganda wanda aka kafa a shekara ta alif dubu biyu da hudu 2004. Shi ne bikin fina-finai mafi dadewa a Uganda wanda masanin tarihin fina-finan Holland Alice Smits da ɗan fim Ba'amurke Lee Elickson suka kafa.[1]
Iri | film festival (en) |
---|---|
Validity (en) | 2004 – |
Wuri | Kampala |
Ƙasa | Uganda |
Yanar gizo | amakula.org |
Tarihi
gyara sasheAn kaddamar da bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na Amakula Kampala na farko a ranar ashirin da daya 21 ga watan Mayu, shekarar alif dubu biyu da hudu 2004. Siffofin bikin Shirin Za a raba shirin nunawa zuwa zaɓaɓɓu waɗanda za a iya ma’anarsu da: Cinema na zamani Binciken fina-finai na yau da kullum na duniya.[2]
Bikin ya ƙunshi gasa, tattaunawa, tarurrukan bita da kuma taron karawa juna sani da sauran wasannin motsa jiki da yawa.[3]
koma baya
gyara sasheBikin ya samu babban koma baya ne a shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2012 wanda a cewar wasu majiyoyin ya faru ne saboda dalilai na kuɗi amma an dawo da shi a ranar goma sha shida 16 ga watan Maris, shekarar alif dubu biyu da goma sha shida 2016 a ƙarƙashin wani sabon gudanarwa, wanda ya tashi daga gidauniyar al’adu ta Amakula zuwa yanzu Gidauniyar Al’adu ta Bayimba ta gabatar.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "About - Amakula". amakula.org. Archived from the original on 26 February 2016. Retrieved 5 June 2018.
- ↑ "Agenda culturel : Tous les événements en Afrique et dans le monde". www.africultures.com. Archived from the original on 2016-02-23.
- ↑ "Agenda culturel : Tous les événements en Afrique et dans le monde". www.africultures.com. Archived from the original on 2016-02-23.
- ↑ "Uganda Amakula Film Festival Returns". artmatters.info. 29 August 2015. Archived from the original on 1 November 2015. Retrieved 5 June 2018.