Aliyu Sani Madaki (An haife shi a ranar 15 ga watan Junairu shekarata alif 1967) a karamar hukumar Dala dake jihar Kano a arewacin Najeriya.

Haihuwa da Karatu

gyara sashe

An haifi Aliyu Sani Madaki ranar 15 ga watan Junairu 1967 a garin Dala dake jihar Kano a Najeriya.

Hon. Madaki ya halarci Makarantar Sakandare ta Gwamnati Gwammaja, Kano inda ya samu shaidar kammala sakandare ta yammacin Afrika (WAEC) a shekarar 1984. Ya wuce Kano State Polytechnic inda ya sami Difloma ta kasa (OND) a shekarar 1987. A lokacin da yake karatu a Kano State Polytechnic. ya kasance shugaban kungiyar dalibai (SUG). Ya halarci Makarantar Koyon Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic Mubi) inda ya karanta Accounting sannan ya kamala digiri na biyu (HND) a shekarar 1987. A shekarar 2015, ya sami digiri na MBA a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi.[1]

Aliyu Sani Madaki ya yi aiki a matsayin akawu a ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya Abuja daga shekarar 1991 zuwa 2001. Sannan ya kasance babban akawunta a ma’aikatar kudi ta tarayya daga 2001 zuwa 2002. A tsakanin 2002 zuwa 2006 ya kasance mataimakin shugaban akawuntan kudi a ma’aikatar kudi ta tarayya. Ma'aikatar Wutar Lantarki da Karfe ta Tarayya. A shekarar 2006 Aliyu ya Ajiye aikin gwamnati inda yakoma rike kamfaninsa mai Suna Madakin gini consults Daga 2007 zuwa 2011 ya kasance Manajan Daraktan Madakin Gini Consults.[2]

A shekarar 2007 Aliyu ya shiga harkar siyasa sosai Inda yayi Takarar majalisar tarayya a karkashin tutar Jam'iyyar AC Amma baiyi Nasara ba.

A shekara ta 2011 ne Madaki ya kuma tsayawa takara a Jam'iyyar PDP inda ya lashe kujerar Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Karamar Hukumar Dala 2011-2015. Daga 2011 zuwa 2015, ya yi aiki a kwamitocin majalisar kamar haka; Housing, Appropriations, Legislative Budget & Research, (Mataimakin Shugaban), Cibiyoyin Lafiya, Harkokin Waje, da kuma Banking & Currency.

An sake zabe shi a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar All Progressive (APC) 2015-2019 Kuma ya tsaya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a shekarar 2019 a karkashin tutar jam'iyyar PDP. Inda yayi rashi nasara a hannun Abokin Takarar sa Tsohon gwamnan Jahar Kano Malam Ibarahim shekarau.[3]

Manazarta

gyara sashe