Aliyah Boston
Aliyah Boston (an haife ta a ranar 11 ga watan Disamba, shekara ta alif dubu biyu da daya 2001)babbar 'yar wasan basketball ce ta kasar Amurka kuma cibiyar Indiana Fever Ƙungiyar basketball ta Mata (WNBA). An saka mata suna a shekara ta alif dubu biyu da a shirin da ukku 2023 WNBA Rookie of the Year a cikin kuri'un da aka kada da kuma AP Rookie of The Year . Ta buga basketball a kwaleji a Jami'ar South Carolina .
An haife ta ne a Saint Thomas, a yanki Virgin Islands a kasar Amurka, Boston ta halarci Kwalejin Worcester a Worcester, Massachusetts, inda ta kasance McDonald's All-American kuma 'yar wasan Massachusetts Gatorade na Shekara sau uku.[1] Boston ta lashe lambobin zinare da yawa da ke wakiltar kasar Amurka.
Boston ta jagoranci South Carolina zuwa gasar zakarun kasa ta biyu a tarihin makaranta a shekara ta alif dubu biyu da a shirin da biyu 2022 kuma an kira ta NCAA Tournament Most Outstanding Player (MOP). A wannan shekarar, ta kuma lashe lambar yabo ta Player of the Year da Defensive Player of the year. Boston ta lashe lambar yabo ta Lisa Leslie a matsayin mafi kyawun cibiyar wasan kwando na mata na NCAA a cikin shekaru hudu a jere.
A ranar 1 ga watan Afrilu, shekara ta alif dubu biyu da a shirin da ukku 2023, Boston ta ayyana Shirin WNBA a shekara ta alif dubu biyu da a shiri da ukku 2023. Boston ta zaɓi ta daina karin shekara ta cancanta da aka ba 'yan wasan koleji saboda annobar COVID-19. [2] Ta ƙare aikinta na shekaru huɗu na kwaleji tare da rikodin nasarori 129 da asarar 9.[3] Boston ita ce na farko da aka zaɓa a cikin shirin WNBA a ranar 10 ga watan Afrilu, shekara ta alif dubu biyu da a shirin da ukku 2023, wanda Indiana Fever ta zaba.[4]
Rayuwa ta farko
gyara sasheAn haifi Boston a ranar 11 ga watan Disamba, shekara ta lif dubu biyu da daya 2001, ga iyayen Cleone da Al a Saint Thomas, a yanki Virgin Islands na kasar Amurka. Boston ta fada cikin soyayyar basketball a lokacin da take da shekaru 9 tana kallon 'yar'uwarta Alexis tana wasa. A lokacin da suke da shekaru 12, Aliyah da Alexis sun ƙaura daga gidansu a yankin Virgin, zuwa New England don zama tare da kawunansu, Jenaire Hodge, da dan uwanta, Kira Punter . Boston za ta ga iyayenta sau da yawa a cikin shekaru masu zuwa, galibi don kallon wasannin kwando na AAU na Aliyah.[5][6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Aliyah Boston". Usab.com. Archived from the original on March 26, 2020.
- ↑ Smith, Jordan C. (15 March 2022). "Academic Impact of COVID-19 in Collegiate Athletes". Kansas Journal of Medicine. University of Kansas Medical Center. 15: 101–105. PMC 8942400 Check
|pmc=
value (help). PMID 35345576 Check|pmid=
value (help). - ↑ Philippou, Alexa (1 April 2023). "South Carolina star Aliyah Boston declares for WNBA draft". ESPN. Retrieved 1 April 2023.
- ↑ "LIVE: Indiana Fever pick Aliyah Boston No. 1 in 2023 WNBA Draft". The Indianapolis Star (in Turanci). Retrieved 2023-04-10.
- ↑ "Far From Home, Aliyah Boston Has Found A Home On The Court With USA Basketball". Archived from the original on August 15, 2020. Retrieved June 18, 2021.
- ↑ "Where will Aliyah Boston take her two gold medals next?". September 27, 2018. Retrieved June 18, 2021.