Alinah Kelo Segobye
Alinah Kelo Segobye 'yar gwagwarmayar ci gaban zamantakewar al'umma ne kuma masaniya a ilimin kimiya na kayan tarihi, tare da ƙwarewa a fannin ci gaban zamantakewa da cutar kanjamau da kuma makomar nazarin abubuwan da suka gabata a Afirka da ilimin kimiya na Afirka.[1] Ita ce Shugabar sashen Kimiyyar Ɗan Adam a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Namibia kuma zaɓaɓɓiyar fellow na Kwalejin Kimiyya na Afirka.
Alinah Kelo Segobye | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Botswana |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Botswana master's degree (en) University of Cambridge (en) 1994) Doctor of Philosophy (en) |
Matakin karatu | Doctor of Philosophy (en) |
Sana'a | |
Sana'a | archaeologist (en) , gwagwarmaya, Farfesa, deputy (en) da shugaba |
Employers |
Jami'ar Botswana Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Namibia |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba | African Academy of Sciences (en) |
Ilimi
gyara sasheSegobye ta kammala karatun digirinta na farko da digiri na biyu a Jami'ar Botswana, kuma ta kammala karatun digiri a Jami'ar Cambridge tare da digiri na uku a fannin Archaeology a shekara ta 1994.[2]
Sana'a
gyara sasheSegobye ta yi aiki a matsayin Mataimakiyar Daraktar a Majalisar Binciken Kimiyyar Ɗan Adam ta Afirka ta Kudu. Daga nan ta yi aiki a Jami'ar Botswana kafin ta shiga aikinta na yanzu a matsayin shugabar Kimiyyar Ɗan Adam a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Namibia.[3] Ta kasance Shugabar Ƙungiyar Archaeological Association ta PanAfrican daga shekarun 2005 zuwa 2010.[4]
Karramawa
gyara sasheSegobye zaɓaɓɓiya ce n'ta Kwalejin Kimiyya na Afirka (2018)[5] kuma farfesa mai daraja a Cibiyar Shugabancin Afirka ta Thabo Mbeki (TMALI), Jami'ar Afirka ta Kudu.[6] Tana aiki a hukumar haɗin gwiwar HIV/AIDS ta Afirka (ACHAP).[7]
An gayyace ta don yin jawabi na biyu na UNESCO Future Forum Africa a shekarar 2013.[1] Ta kasance malama mai ziyara a Bradford Rotary Peace Center (2016).[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "UNESCO Future Forum Africa #2: Decolonizing African Futures: Exploring and Realigning Alternative Systems" (PDF). UNESCO. 6 December 2013.
- ↑ Townsend, Leonie. "Prof Alinah Kelo Segobye". Welcome to Foresight For Development (in Turanci). Retrieved 2020-02-27.
- ↑ "Alinah Segobye | Faculty of Human Sciences". fhs.nust.na (in Turanci). Archived from the original on 2020-10-31. Retrieved 2020-02-27.
- ↑ "Congresses and Presidents – PanAfrican Archaeological Association". www.panafprehistory.org. Archived from the original on 2022-12-01. Retrieved 2021-10-22.
- ↑ 5.0 5.1 "Segobye Alinah Kelo | The AAS". www.aasciences.africa. Archived from the original on 2020-02-27. Retrieved 2020-02-27.
- ↑ "Alinah Kelo Segobye". The Conversation (in Turanci). 25 May 2015. Retrieved 2020-02-27.
- ↑ "Welcome to ACHAP". www.achap.org. Archived from the original on 2020-02-10. Retrieved 2020-02-27.