Albachir Mouctar
Albachir Mouctar (an haife shi 1 ga Mayu shekarar 1996)[1] ɗan wasan ninƙaya ne na ƙasar Nijar. Ya wakilci ƙasarsa a gasar Olympics ta bazara ta 2016 a cikin gasar tseren mita 50 na maza inda ya kasance a matsayi na 70 tare da lokacin daƙiƙa 26.56, rikodin ƙasa. Bai kai matakin wasan kusa da na ƙarshe ba.
Albachir Mouctar | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Nijar |
Shekarun haihuwa | 1 Mayu 1995 |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | swimmer (en) |
Wasa | ninƙaya |
Participant in (en) | swimming at the 2016 Summer Olympics (en) |
Albachir kuma shi ne ke riƙe da kambun ƙasa a Nijar a tseren mitoci 50 na maza.
A shekarar 2019, ya wakilci Nijar a gasar cin kofin Afirka na 2019 da aka gudanar a Rabat, Morocco.[2]