Ajoritsedere (Dere) Josephine Awosika ƴar kasuwa ce ƴar Najeriya wacce ta zamo shugabar bankin Access Plc.[1] Kafin a bata wannan matsayin, ta kasance Sakatariya ta dindindin a Ma’aikatun Cikin Gida, Kimiyya da Fasaha da Makamashi na Tarayya a lokuta daban-daban.

Ajoritsedere Awosika
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi mace

Farkon rayuwa gyara sashe

An haifi Awosika a garin Sapele, itace ‘ya ta shida ga ministan Kuɗin Najeriya na farko a jamhuriya ta farko wato Festus Okotie-Eboh, wadda aka kashe a cikin shekarar 1966.[2][3] Ta kasance ma'aikaciyar ƙungiyar Magunguna ta Najeriya da kuma Kwalejin Kimiyya ta Yammacin Afirka ta Yamma. Tsohuwar dalibar Jami'ar Bradford ce, inda ta sami digiri na uku a fannin fasahar magunguna.

Manazarta gyara sashe

  1. "Dr. Ajoritsedere Awosika". Archived from the original on 3 September 2022. Retrieved 3 September 2022.
  2. "The many misconceptions about my father, Festus Okotie-Eboh —Dere Awosika, daughter". Retrieved 18 April 2020.
  3. "My father warned the Prime Minister they would all be killed–Awosika, Festus Okotie-Eboh's daughter". Retrieved 18 April 2020.