Aisha Abimbola (An haife ta 19 ga watan Disamba, shekara ta 1970 - Ta muta 15 ga watan Mayu, shekarar 2018), an haife ta a Epe, Jihar Legas, ta kasance 'yar fim din Najeriya kuma tauraruwar fina-finan Yarbanci.

Aisha Abimbola
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 1974
Mutuwa 2018
Sana'a

Rayuwar Farko da Ilimi gyara sashe

Abimbola ta kasance musulma amma sai ta juya zuwa Kiristanci wanda ta kasance a sauran rayuwarta. Ta taba fada a wata hira da ta yi da New Telegraph cewa da ta zama fasto idan ba ta shiga harkar fim ba. Aisha Abimbola ta auri Victor Ibrahim Musa kuma sun haifi yara biyu. Aisha ta halarci karatunta na sakandare a Ebute Elefun High School kuma ita ce Head girl a set din 1994’. Bayan haka, ta ci gaba da zuwa Kwalejin Fasaha ta Jihar Legas (LASPOTECH) inda ta samu shaidar kammala da da matsayin diploma (HND) inda ta karanta bangaren girke-girke da kuma abinda ya shafa hotel.

Fina-finanta gyara sashe

  • No Pain
  • No Gain
  • Awerijaye
  • So Wrong So Right
  • Omoge Campus
  • Kamson and Neighbours

Manazarta gyara sashe

http://www.nigerianmonitor.com/aisha-abimbola-biography-profile-nigerian-monitor/ Archived 2020-11-17 at the Wayback Machine