Aisha (1953 fim)
Aisha fim ne na wasan kwaikwayo na kasar Masar a 1953 wanda Gamal Madkoor ya bada umarni. Tauraruwar ta hasashe Zahrat El-Ola, Zaki Rostom, da Faten Hamama.[1][2]
Aisha (1953 fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1953 |
Asalin suna | عائشة |
Asalin harshe | Larabci |
Ƙasar asali | Misra |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
Launi | black-and-white (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Gamal Madkoor (en) |
'yan wasa | |
Faten Hamama (en) | |
External links | |
Specialized websites
|
Labari
gyara sasheWani attajiri ya haɗu da wata talaka mai suna Ai'sha mai sayar da tikitin caca a kan titi. Yana mamakin yadda kamanninta ya yi kama da na ɗiyarsa da ta rasu kwanan nan. Attajirin ya ba wa mahaifinta kuɗin wata-wata don ya karɓe ta. Baban ya karɓa, bayan ya gano yadda attajirin ke da alaƙa da Ai'sha, sai mahaifin ya yi ƙoƙarin yi masa baki don neman ƙarin kuɗi. Ƴan sanda sun gane, suka ɗaure mahaifin.
An sake shi daga gidan yari ya tarar da A’isha ta kammala karatun ta. Ya nemi kuɗi masu yawa daga wurin attajirin, amma sai ya ƙi yin haka, mahaifin ta ya kama ta da ƙarfi. Fim ɗin ya ƙare ne yayin da A'isha ta koma wajen mahaifinta ta auri soyayyarta, Dr. Sami.
Magana
gyara sasheHanyoyin haɗi na waje
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ http://www.fatenhamama.com/Arabic/films/AISHA.html
- ↑ Film summary, Faten Hamama's official site. Retrieved on 23 January 2007.