Ahmed Aly Ahmed Daador ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Masar wanda ke taka leda a ƙungiyar Pyramids ta Premier ta Masar a matsayin mai tsaron gida.[1][2]

Tarihin rayuwa

gyara sashe

An haifi Ahmed Daador a ranar 10 ga Afrilu 1995[3][2] Ya fara aikinsa a shekarar 2015 da Misr lel-Maqasah SC. A cikin 2017, ya shiga Pyramids FC kuma a cikin 2020 an canza shi zuwa Al Masry. A cikin 2021, an mayar da shi Pyramids FC.[4][5][2]

Ya kasance a cikin tawagar da ta zo ta biyu da ta lashe kofin EFA na 2018/2019 da 2019/2020 CAF Confederation Cup[2]

Manazarta

gyara sashe