Ahmed Baba Kaita
Ahmed Baba Kaita, ɗan siyasan Najeriya ne kuma Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa a karo na biyu. Ya kasance dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Kusada/Ingawa da kuma Kankia a jihar jihar Katsina.[1]
Ahmed Baba Kaita | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Sana'ar siyasa
gyara sasheAn zabi Kaita a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar katsina mazabar Kusada/Ingawa/Kankia a majalisar tarayya inda ya tsaya takara har zuwa shekarar 2018 a lokacin da ya tsaya takarar Sanatan Katsina ta Arewa bayan rasuwar Sanata Mustapha Bukar mai wakiltar gundumar. Kaita ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar All Progressives Congress, APC bayan ya doke sauran 'yan takara 10. Ya ci gaba da lashe babban zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Agustan shekarar 2018, inda ya samu kuri’u 224,607 inda ya doke babban yayansa kuma dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP Kabir Baba-Kaita wanda ya samu kuri’u 59,724. Shugaban majalisar dattawa Bukola Katsina Saraki ne ya rantsar da shi a zaman majalisar dattawa ta 8 a ranar 10 ga watan Oktoba na shekara ta 2018.[2]
Baba-Kaita ya sake lashe zaben majalisar dattawa a shekarar 2019 bayan ya samu scataren kuri’u 339,438 inda ya doke ‘yan takarar jam’iyyar PDP Mani Nassarawa wanda ya samu kuri’u 127,529 da Accord Party Lawal Nalado wanda ya samu kuri’u 14,152. [3] Baba-kaita ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da gwagwalad manyan makarantu da asusun tallafawa manyan makarantu, (TETFund) a majalisar dattawa ta 9.[4][5] Baba-Kaita, Sanata mai wakiltar mazabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a majalisar dattawa ya soki yadda shugaban kasa ya yi a zauren majalisar dattijai musamman kan tabarbarewar tsaro a arewa.[6][7][8] A watan Afrilun 2022, Baba-Kaita ya bayyana ficewarsa daga APC ya koma PDP [9] inda ya nemi tikitin komawa majalisar dattawa amma dan takarar APC Nasir Zangon-Daura ya sha kaye. Baba-Kaita ya samu kuri’u 163,586 inda ya zo na biyu bayan wanda ya lashe zaben, Nasir Zangon-Daura wanda ya samu kuri’u 174,062. A lokacin zaben, Baba-Kaita ya yi wa Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP kamfen ya ci gaba da zama shugaban kasa a Arewa don yakar yankin Kudu maso Kudu bayan jiharkatsina shekaru takwas na Shugaba Buhari daga Arewa.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Reporters, Our (2021-02-13). "2023: Without zoning, APC is doomed – Senator Kaita". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-04-28.
- ↑ "Saraki swears in two new APC senators". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-10-10. Archived from the original on 2023-04-28. Retrieved 2023-04-28.
- ↑ "Senator Babba Kaita Returns to Senate – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2023-04-28.
- ↑ Lamino (2022-09-01). "TETFund: Senate seeks increase in companies tax remittance to boost research". FRCN HQ (in Turanci). Archived from the original on 2023-04-28. Retrieved 2023-04-28.
- ↑ Akinyemi, Femi (2022-09-01). "TETFund: Senate committee seeks increase of education tax to boost research". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-04-28.
- ↑ "Insecurity: Buhari's efforts not good enough, says Katsina senator". TheCable (in Turanci). 2020-12-01. Retrieved 2023-04-28.
- ↑ "Terrorists abduct wife of senator Baba Kaita's younger Brother, 2 children in Katsina | AIT LIVE". ait.live (in Turanci). 2022-08-08. Retrieved 2023-04-28.
- ↑ "Terrorists Kidnap Wife Of Senator Baba-Kaita's Younger Brother, 2 Children In President Buhari's Home State, Katsina | Sahara Reporters". saharareporters.com. Retrieved 2023-04-28.
- ↑ Online, The Eagle (2022-04-21). "Senator representing Buhari's District dumps APC -". The Eagle Online (in Turanci). Retrieved 2023-04-28.