Adedoyin Salami
Rayuwa
Haihuwa 4 ga Afirilu, 1963 (61 shekaru)
Karatu
Makaranta Queen Mary University of London (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki da Malami
Employers Jami'ar jahar Lagos

Adedoyin Salami (An haife shi a ranar 4 ga watan, Afirilu shekara ta 1963). masanin tattalin arzikin Najeriya ne wanda a halin yanzu shine babban mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan tattalin arziki .

An haifi Adedoyin Salami a ranar 4 ga watan Aprilun shekara ta, 1963.

Shi babban abokin aiki ne kuma mataimakin farfesa a Makarantar Kasuwancin Legas na Jami'ar Pan-Atlantic. Ya fara aiki da Adetutu & Co kafin ya shiga Jami'ar Legas a matsayin malami a Sashin Tattalin Arziki. Ya kasance memba a kwamitin kula da harkokin kudi na babban bankin Najeriya daga shekarar, 2010 zuwa 2017.[1]

A shekarar, 1989 yayi Digirin digirgir a fannin Tattalin Arziki a Kwalejin Sarauniya Mary, Jami'ar London, Bukatun binciken Adedoyin Salami ya haɗa da batutuwan kula da harkokin kuɗi na dogon lokaci; manufofin tattalin arziki; gasar kamfanoni da gudanarwa da haɗari; da halaye na Kananan da Matsakaicin kasuwanci (SMEs). Shi ne shugaban majalisar ba da shawara kan tattalin arziki da shugaba Buhari ya kafa, mai kai rahoto kai tsaye. [2]

Sana'a/Siyasa

gyara sashe

Yayi karantarwa a jami’ar Legas, Adedoyin ya gina cibiyar bada shawara, da kuma kamfanin bincike Edward Kingston Associates a shekarar, 1997, wanda ya hada da Soft skills a shekarar, 2014 ya kafa Kainos Edge. Memba ne a tsangayar koyarwa ta Makarantar Kasuwancin Legas (LBS), Jami'ar Pan — Atlantic inda yake jagorantar zaman tattalin arziki na Kasuwanci. Kafin ya shiga LBS, Adedoyin ya kasance Manajan Partner na Edward Kingston Associates, wani kamfani mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki, inda ya jagoranci wata tawaga ta gina Model na Macroeconomic na tattalin arzikin Najeriya. Sauran ayyukan tuntubar sa sun hada da ayyuka na Coca-Cola Nigeria da Equatorial Africa (CCNEAL), Department for International Development (DFID), Bankin Duniya, Majalisar Dinkin Duniya Cibiyar Raya Masana'antu (UNIDO), Hukumar Raya Kasa da Kasa ta Amurka (USAID) ) da kuma yin aiki a matsayin Mai bita na Abokin Hulɗa na Ƙungiyar Kuɗi ta Duniya (IFC) game da dabarun Najeriya.[3]

Shigar sa a fannin Siyasa ya fara ne a shekarar, 2009 inda Marigayi Shugaba ‘Yar-Adua ya nada shi a matsayin mamba a kwamitin kula da tattalin arzikin Najeriya. A shekarar, 2010, an nada shi mamba a kwamitin kula da harkokin kudi (MPC) na babban bankin Najeriya ya kuma yi ritaya daga MPC a shekarar, 2017 bayan ya kammala wa’adi biyu. Adedoyin ya kuma taba zama mataimakin shugaba (karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Joda) na kwamitin mika mulki na shugaban kasa Muhammadu Buhari. Memba na Kungiyar Bada Shawarwari ta Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) don Yankin Saharar Afirka (AGSA),shi ma memba ne na Hukumar Tattalin Arziki ta Najeriya (NESG) kuma yana da damar kasancewa Co. -Shugaban kwamitin tsakiya na babban taron tattalin arzikin Najeriya a shekara ta, 2009. [4]

Adedoyin yayi rubuce-rubuce da dama akan tattalin arzikin Najeriya. Kuma a halin yanzu yana zaune a kan ma'aikar African Business Research Ltd., First World Communities, da Diamond Pension Fund Custodian.

Shugaban PEAC

gyara sashe

A ranar 16 ga watan Satumba a shekara ta, 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya naɗa shi a matsayin shugaban sabuwar majalisar ba da shawara kan tattalin arzikin kasa (PEAC), wacce za ta kai rahoto ga shugaban kasa kai tsaye.

A watan Janairun shekara ta, 2022, fadar shugaban Najeriya ta sanar da amincewa da naɗin Dakta Doyin Salami a matsayin babban mai baiwa Muhammadu Buhari shawara kan tattalin arziki. Har zuwa lokacin shi ne shugaban kwamitin tuntubar tattalin arziki na shugaban kasa (PEAC).[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bbc.com/pidgin/world-59872212
  2. https://www.premiumtimesng.com/news/more-news/504495-profile-doyin-salami-buharis-new-economic-adviser.html
  3. https://www.nairaland.com/5420762/biography-profile-adedoyin-salami-chairman
  4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-06-29. Retrieved 2022-06-24.