Abubakar Yahaya Kusada
Abubakar Yahaya Kusada ɗan siyasan Najeriya ne kuma ɗan majalisa daga jihar Katsina a Najeriya. An haife shi a ranar 25 ga watan Disamba 1979.
Sana'a
gyara sasheHon. Abubakar Yahaya Kusada ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai ta tarayya a jihar Katsina, mai wakiltar mazaɓar Kankiya/Kusada/Ingawa daga shekarun 2019 zuwa 2023. [1] A lokacinsa ya kaddamar da ayyuka da dama a mazaɓar sa a ƙarƙashin jam’iyyar APC. [2] Waɗannan ayyuka sun haɗa da gina rijiyoyin burtsatse a cikin al’umma kamar Kwana, Kafin Soli, Gidan Kusa, Fanfarauta, da Dundu. Ya kuma gina makarantu tare da samar da kayan aiki, ya karfafa matasa, da sauran su. Kusada ya kuma riƙe wasu muƙamai na siyasa kuma mamba ne a Cibiyar Kula da Kididdigar Ƙasa ta Najeriya da Hukumar Rijistar Kuɗi. [3] [4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-13.
- ↑ "Katsina state House of Representatives election results and data 2023 - Stears Elections". www.stears.co. Retrieved 2024-12-13.
- ↑ News, Katsina City. "Works, Achievements, Successes Of Abubakar Yahaya Kusada Within The Last Six Months". www.katsinatimes.com (in Turanci). Retrieved 2024-12-13.
- ↑ "Meet Katsina newly elected member, House of Representatives - Daily Trust". dailytrust.com/ (in Turanci). 2018-11-18. Retrieved 2024-12-13.