Abu Salih as-Samman (Larabci: أبو صالح السمان) (ya rasu AH 101, CE 720) shi ne farkon malamin addinin musulunci na Madina. Ya kuma kasance mai riwayar Hadisi yana daga cikin tsarar Tabi'un musulmi.

Abu Salih as-Samman
Rayuwa
Sana'a
Sana'a muhaddith (en) Fassara

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haife shi a zamanin Umar bin Al-Khattab, kuma bawan Juwairiyya ne ‘yantacce – matar Annabi Muhammad.[1] Ya zauna a madina, ya kuma shaida wa Usmanu hari. Ya rasu a shekara ta 101 bayan hijira a ƙarshen mulkin Umar bin Abdil-Aziz.[2]

Ya hadu da da yawa daga cikin sahabban Muhammad, kuma ya ruwaito hadisi daga:

Wasu daga cikin mutanen da suka ruwaito daga gare shi sun hada da:

  • Sohail ibn Abi Saleh (ɗa)
  • Sulaiman Al-A’mash
  • Zayd ibn Aslam
  • Abdullah ibn Dinar
  • Ibn Shihab al-Zuhri

Ahmad ibn Hanbal ya ce ana yi masa kallon Thiqa, (amintaccen abin da ya shafi hadisi) kuma ya shahara da daraja.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 Al-Dhahabi. Siyar a`lam al-nubala (in Arabic). p. 172.CS1 maint: unrecognized language (link)
  2. Ibn Kathir. Bidayah wa al-Nihayah (in Arabic). 12. p. 723. وفيها توفي مع عمر بن عبد العزيز ربعي بن حراش، ومسلم بن يسار وأبو صالح السمانCS1 maint: unrecognized language (link)
  3. Bukhari. al-Tārīkh al-Kabīr. 3. p. 260.
  4. Ibn Hibban. Al-Thiqat (in Arabic). p. 222.CS1 maint: unrecognized language (link)