Abokan wasa
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Abokan wasa Ba wai ana nufin abokan da muke wasa dasu ba, ko abokanmu na yarinta, ko abokan da muke gobza wasa a rukuni ba, Abokan wasa a al'adar bahaushe wasu mutane ne a dangi wanda muka hada wata alaka ta jini dasu ta dalilin iyayen maza ko iyayen mata. A wannan mukala zanyi takaitaccen bayani ne akan wadannan mutane wanda suke a matsayin abokan wasan al'adar malan Bahaushe.
Su waye abokan wasa
gyara sasheAna samun abokan wasa ta bangare biyu,bangaren mahaifi da kuma ɓangaren mahaifiya. Bangaren Mahaifi :- ƴaƴan Gwaggonka wato kanwa ko yayar mahaifi sune abokan wasan ka/ki. Bangaren Mahaifiya= Ƴaƴan kawu wato yayu ko kannan mahaifiya sune abokan wasan ka/ki.