Abid el gassad
Abid el gassad ( Larabci: عبيد الجسد ) fim ne na shekarar 1962 wanda Kamal Atia ya bada Umarni. Taurarin shirin sun haɗa da Huda Sultan, Farid Shawqi, Mahmoud Al Meleji, Tawfik El Deken, da Shafik Nour El Din.
Abid el gassad | |
---|---|
Asali | |
Ƙasar asali | Misra |
Characteristics | |
Direction and screenplay | |
Darekta | Kamal Attia (en) |
'yan wasa | |
External links | |
Specialized websites
|
Makirci
gyara sasheFim ɗin ya ta'allaka ne akan Abd al-Fattah, wanda ya saci buhun kudi na "Uncle Amin" a lokacin da yake wajen wani shago da ƴar kasuwa mai suna "Samia" ke aiki. Samia ta ɗauki hoton satar da aka yi kuma ta yanke shawarar cewa za ta yi barazanar mayar wa barawon jakar, ko kuma ta kai kararsa ga ƴan sanda. An samu saɓani tsakanin “Ali” da ƴan uwansa ɓarayin dangane da mayar da jakar ga mai ita. Fim ɗin ya biyo bayan ci gaban wani labarin soyayya ne tsakanin Ali da Samia, inda suka fita tare kuma a karshe suka yanke shawarar yin aure, bisa sharadin Ali ya bar rayuwarsa ta aikata laifuka. Sannan Samia tana aiki a matsayin ma'aikaciyar ajiya a wani ƙaramin shago.
Yan wasan kwaikwayo
gyara sashe- Huda Sultan a matsayin Samia/Wafaa
- Mahmoud Al Meleji a matsayin Ahmed Hassan
- Farid Shawqi a matsayin Ali Abd al-Fattah
- Tawfik El Deken a matsayin memba na kungiyar Ali Abd al-Fattah
- Shafik Nour El Din a matsayin Uncle Amin
- Zahia Ayoub a matsayin matashiya Layla Ali Abd al-Fattah
- Zeinat Olwi a matsayin mai rawa
- Abdel Hamid Badawi a matsayin Uncle Refa'i Al-Farash
- Fathia Shahin a matsayin mai kula
- Mohsen Hosny a matsayin memba na kungiyar Ali Abd al-Fattah
- Abdul Ghani Al-Najdi a matsayin mai kayan ado
- El Tawky Tawfik a matsayin memba na ƙungiya
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Abid el gassad on IMDb
- عبيد الجسد on ElCinema