Abdulwahab Abdullah

Malamin addinin musulunci ne

Shaikh Abdulwahab Abdullah fitaccen Malami ne na addinin musulunci mazaunin garin Kano a Najeriya.

Abdulwahab Abdullah
Rayuwa
Haihuwa 28 ga Augusta, 1953 (70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a scholar (en) Fassara
Malam ko Mai tafsir

Farkon Rayuwa gyara sashe

 
Fitaccen malamin addinin musulunci mai suna Shaikh Abdulwahab Abdullah mazaunin garin Kano a Nijeriya.

Shaikh Abdulwahab Abdullah, An haife shi ne a ranar 28 ga watan Agusta na shekarar alif dari tara da hamsin da uku 1953, wanda ya yi dai dai da ranar Juma’a 17 ga watan Zul-Hijjah shekara ta alif dari uku da saba'in da uku 1373 Miladiyya, a ƙasar Togo.[1]

Karatu gyara sashe

Shaikh Abdulwahab Abdullah Ya soma karatu a wurin yayan mahaifinsa mai suna Imam Alhaji Yahya. Daga bisani ya yi karatu a wurin babban malami marigayi Imam Ɗan’ammu da ke birnin Kano. Kazalika ya kuma yi karatu a wurin Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Shehu Maihula da gidan Shamsu inda akwai malamai irin su Malam Gali, da Malam Babba.[2]

Zuwa Saudiyya gyara sashe

Bayan karutunsa a jihar Kano Najeriya, daga nan ne ya tafi Saudiyya tare da matarsa inda ya yi karatu a can. Malam ya yi karatu a wurin Sheikh Bn Bazz da Sheikh Uthaimin, waɗanda ya ce ya koyi halaye na gari da matuƙar tsoron Allah a wurinsu.[3]

Manazarta gyara sashe