Abdellatif Ben Ammar ( Larabci: عبد اللطيف بن عمار‎ 25 Afrilu 1943 - 6 Fabrairu 2023) darektan fina-finan Tunisiya ne kuma marubucin fim.[1]

Abdellatif Ben Ammar
Rayuwa
Haihuwa Tunis, 25 ga Afirilu, 1943
ƙasa Tunisiya
Mutuwa Tunis, 6 ga Faburairu, 2023
Karatu
Makaranta Alaoui Lyceum (en) Fassara
Institut des hautes études cinématographiques (en) Fassara
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a darakta da marubin wasannin kwaykwayo
IMDb nm0069888
Abdellatif Ben Ammar

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haife shi a birnin Tunis a ranar 25 ga watan Afrilu 1943, Ben Ammar ya karanci fannin ilimin lissafi a Lycée Alaoui [fr]. Daga nan ya koma harkar cinema kuma ya sami difloma a harkar fim daga Institut des haute études cinématographiques a birnin Paris a shekarar 1965.

Bayan ya koma Tunisiya, Ben Ammar ya samu hayar kamfanin Tunisiya don shirya fina-finai da faɗaɗawa kuma ya fara ɗaukar gajerun fina-finai tare da taimakon daraktocin Tunisiya da na waje. A cikin shekarar 1970, ya fito da fim ɗinsa na farko, Labari Mai Sauƙi, sannan ya kafa kamfanin studio Latif Productions tare da Abdellatif Layouni. Ya kuma yi haɗin gwiwa wajen kafa kamfanin post-production Company, Ben Duran.

 

Ben Ammar ya mutu a birnin Tunis a ranar 6 ga Fabrairu, 2023, yana da shekaru 79 a duniya.

Fina-finai

gyara sashe
  • 2 + 2 = 5 (1966)
  • Le Cerveau (1967)
  • Opération yeux (1967)
  • L'Espérance (1968)
  • A Simple Story (1970)
  • Sur les traces de Baal (1971)
  • Mosquées de Kairouan (1972)
  • Samfuri:Ill (1973)
  • Sadiki (1975)
  • Kairouan, la Grande Mosquée (1979)[2]
  • Aziza (1980)
  • Le Chant de la noria (2002)
  • Farhat Hached (2002)
  • Khota Fawka Assahab (2003)
  • Les Palmiers blessés (2010)

Distinctions

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "ʻAmmār, ʻAbd al-Raḥmān, 1943-". Library of Congress.
  2. Nasser Sardi, Mohamed (25 April 2007). "Les journées du cinéma tunisien (J.C.T.). Deuxième session". Africiné (in French). Retrieved 7 February 2023.CS1 maint: unrecognized language (link)