An gudanar da kuri'ar raba gardama kan zama yankin Najeriya a Arewacin Kamaru a watan Nuwamba 1959.[1] An bai wa masu kada kuri’a zabi tsakanin wata kungiya da Najeriya da kuma dage matakin.[1] Masu jefa kuri'a sun goyi bayan na biyu,inda kashi 62.25% suka kada kuri'ar dage yanke shawarar.[1] An gudanar da zaben raba gardama karo na biyu a shekarar 1961,inda kashi 60% suka kada kuri'ar shiga Najeriya sannan kashi 40% suka kada kuri'ar shiga Kamaru.[1]
Zabi
|
Ƙuri'u
|
%
|
</img> Dage yanke shawara
|
70,546
|
62.25
|
Hadin kai da Najeriya
|
42,788
|
27.75
|
Kuri'u marasa inganci/marasa kyau
|
525
|
-
|
Jimlar
|
113,859
|
100
|
Masu jefa ƙuri'a / masu yin rajista
|
129,549
|
87.9
|
Bayanan Zabukan Afirka
|