Zineb Oukach
Zineb Oukach (Larabci: زينب أوكاش an haife ta a ranar 4 ga watan Janairu 1993) 'yar wasan fina-finan Morocco ce kuma abar koyi, sananniya ga masu sauraro a duniya a rawar da taka a matsayin Fatima a cikin fim ɗin Gavin Hood na 2007 Rendition.[1]
Zineb Oukach | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Casablanca, 1 Disamba 1982 (42 shekaru) |
ƙasa | Moroko |
Harshen uwa | Larabci |
Karatu | |
Makaranta | Cours Florent (en) |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | model (en) da jarumi |
IMDb | nm2796785 da nm3274358 |
zineboukach.com |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Oukach kuma ta girma a Casablanca, Maroko. A shekara ta 2004 ta koma Faransa, inda ta yi karatun tattalin arziki kafin ta halarci Cours Florent don mai da hankali kan aikin wasan kwaikwayo.[1]
Sana'a
gyara sasheAn riga an san ta a Maroko don aikinta a Parfum de Mer, wanda fitaccen mai shirya fina-finan Morocco Abdelhai Laraki ya yi, da kuma rawar da ta taka a cikin jerin talabijin na Moroccan Une Famille Respectable na Kamal Kamal, a shekarar 2007 Oukach ya yi suna a duniya saboda rawar da ta taka tun tana matashiya. Balarabe ta jagoranci fim ɗin Rendition tare da Meryl Streep, Jake Gyllenhaal da Reese Witherspoon. Oukach kuma ta taka rawa a cikin Wolf of Wall Street.[1] Kuma a cikin jerin almara na kimiyya Alien Dawn, wanda aka watsa akan Nickelodeon.
Filmography
gyara sashe- Rendition - Fatima (2007)
- (French title: Détention secrète)
- Parfum de Mer - Nadia (2006)
- (English title: Scent of the Sea)
- The Wolf of Wall Street - hostess on yacht (2013)
- ’’Alien Dawn’’ - Stella
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Zineb Oukach". Movies & TV Dept. The New York Times. Baseline & All Movie Guide. 2015. Archived from the original on 2015-06-30.