Happiness Biyela (an haife ta a ranar 24 ga watan Fabrairun shekara ta 1983), wacce aka fi sani da Zim Dollar, ƴar wasan kwaikwayo ce ta Afirka ta Kudu, mai gabatar da shirin talabijin, mawaƙiya, MC, DJ na rediyo kuma mai karfafa gwiwa.[1] An fi saninta da rawar da ta taka a cikin shirye-shiryen talabijin kamar; Uzalo , Durban Gen da eHostela.[2][3]

Rayuwa ta mutum gyara sashe

An haifi Biyela a ranar 24 ga Fabrairu 1983 a eNdabazensangu a ƙarƙashin Gundumar Sarki Cetshwayo, Obuka, Afirka ta Kudu a matsayin ɗaya daga cikin tagwaye da na uku a cikin iyali tare da 'yan uwa shida. Ta kammala karatun firamare daga makarantar firamare ta St Paul a Nkwenkwe. Daga nan sai halarci makarantar sakandare ta Sitheku don karatun sakandare kuma ta shiga makarantar a shekara ta 2001. Bayan nan sai ta tafi neman digirin farko a fannin ilimi daga Jami'ar Afirka ta Kudu (Unisa). Ta yi karatu na shekaru biyu a Jami'a, amma ba ta kammala digirin ba.[4]

Tana da ɗa da ta haifa ranar 16 ga watan Afrilu 2007

Manazarta gyara sashe

  1. "Zimiphi Biyela Biography". Savanna News (in Turanci). 2020-10-08. Retrieved 2021-11-13.
  2. styleyou (2021-09-30). "Zimiphi Biyela actress currently caused commotion with her breathtaking beauty on social media". style you 7 (in Turanci). Retrieved 2021-11-13.
  3. Madibogo, Julia. "Grass too green as deejay, worker fight over pay". Citypress (in Turanci). Retrieved 2021-11-13.
  4. "Multi-talented Biyela hungry for gangster role". SowetanLIVE (in Turanci). Retrieved 2021-11-13.