Open main menu
Zaragoza.

Zaragoza (lafazi: /zaragoza/) birni ce, da ke a yankin Aragon, a ƙasar Ispaniya. Babban birnin Aragon ce. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2016, jimilar mutane 661,108 (dubu dari shida da sittin da ɗaya da dari ɗaya da takwas). An gina birnin Zaragoza a ƙarshen karni na ɗaya kafin haifuwan annabi Issa.