Zaizayar ƘasarGundumar Kasese ta 2022
A daren 6 da 7 ga watan Satumbar 2022, [1] mutane 15 ne suka mutu lokacin da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa zabtarewar ƙasa da dama a gundumar Kasese na Uganda . [2]
| ||||
Iri | aukuwa | |||
---|---|---|---|---|
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ne ya haddasa zaftarewar ƙasa. Wurin da ke tudu yana da nisa kuma musamman yana da rauni ga zabtarewar ƙasa.[3]
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Uganda ta tabbatar da cewa akasarin waɗanda suka mutu mata ne da yara. A ƙalla mutane 18 ne aka bayyana bacewarsu sannan a kalla 7 sun jikkata kuma an kai su asibiti.[4]
An lalata gidaje da dama kuma an binne mutane da dama da ransu, tare da ƙoƙarin ceto wanda ya maida hankali kan waɗanda har yanzu ke maƙale a ƙarƙashinsu.[5]
Bayan afkuwar lamarin, a ranar da yamma aka fara shirin miƙa gawarwakin zuwa makarantar firamare ta Kasika domin yi mata rasuwa da kuma shirye-shiryen binne gawa.[6]
Taron ya kasance ɗaya daga cikin jerin ambaliyar ruwa na baya-bayan nan a Yammacin Uganda [7] kuma ɗaya daga cikin da yawa a Afirka a cikin shekarar 2022 .
Manazarta
gyara sashe- ↑ Kazibwe, Kenneth (September 7, 2022). "Uganda: Kasese Landslide Death Toll Rises to 15". allAfrica.com. Archived from the original on September 7, 2022. Retrieved September 7, 2022.
- ↑ Heavy rains trigger landslides in Uganda, killing least 15, Reuters, 7 September 2022, archived from the original on 2022-09-07, retrieved 2022-09-07
- ↑ Muhumuza, Rodney (September 7, 2022). "Red Cross: Landslide kills 15 in remote Uganda district". WKMG. Archived from the original on September 7, 2022. Retrieved September 7, 2022.
- ↑ "15 people perish in fresh Kasese landslides". September 7, 2022. Archived from the original on September 7, 2022. Retrieved September 7, 2022.
- ↑ "15 perish in fresh Kasese landslides. Uganda Redcross society has confirmed". September 7, 2022. Archived from the original on September 7, 2022. Retrieved September 7, 2022.
- ↑ "Kasese deadly landslide death toll rises to 15". September 7, 2022. Archived from the original on September 7, 2022. Retrieved September 7, 2022.
- ↑ "Uganda – 15 Killed in Massive Landslide in Kasese – FloodList". floodlist.com. Archived from the original on 2022-09-07. Retrieved 2022-09-07.