Zainab Ummaru Musa Yar'adau itace uwar gidan Usman Sa'idu Dakin Gari tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, asalin sunan ta shine Zainab Ummaru Musa Yar’adua. Ita yace ga marigayi tsohon Shugaban Kasa Alhaji Umaru Musa Yar'Adua. An haife ta a ranar 1 ga watan Oktoba, shekara ta 1979, a Jihar Katsina.[1]

Tayi makarantar firamare a Katsina Steel Rolling Staff School daga shekarar (1989) zuwa shekarar (1992). Tayi sakandire a kwalejin tarayya ta mata wato Federal Government Girls Day College Bakori daga shekarar (1993 ) zuwa shekarar (1996). Tayi kuma Essence International School, Kaduna daga shekarar (1996) zuwa shekarar (1999). Tayi Jami’ar Maiduguri daga shekarar ( 2000 ) zuwa shekarar (2002 ) inda daga bisani tayi Huron University, London daga shekarar( 2003) zuwa shekarar (2006). Ta kuma yi Project Management College United Kingdom.[1]

Ta buɗe ƙungiya taimakon mata da yara wacce ake kira ‘(ZADAF FOUNDATION FOR WOMEN AND CHILDREN)’.[1]

  • Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.p 173 ISBN 978-1-4744-6829-9.