Zad al-Ma'ad Fi Hadyi Khair Al 'Ibaad (Larabci: زاد المعاد في هدي خير العباد‎ </link>) littafi ne mai juzu'i 5, wanda aka fassara shi a matsayin Shaidar Lahira a cikin Shiryar da Mafificin Bayi, wanda malamin addinin Musulunci Ibn al-Qayyim ya rubuta. Kalmar ‘Zad’ a harshen Larabci ana amfani da ita wajen yin nuni ga abincin da mutum zai ci lokacin da zai fara tafiya, kuma an rubuta littafin yana mai nuni da shiriya daga rayuwar Annabi Muhammadu (S.A.W) wanda musulmi za su iya amfana da shi a tafiyarsu ta rayuwa. Bugu da ƙari, Ibn Al Qayyim ya rubuta littafin a lokacin da yake tafiya.

Zad al-Ma'ad
Asali
Mawallafi Ibn Qayyim al-Jawziyya
Characteristics
Harshe Larabci

Littafin ya kunshi batutuwa da dama, inda marubucin ya fara magana a kan sifofin Annabi Muhammadu (S.A.W), inda ya yi bayani dalla-dalla game da ibadarsa da rayuwarsa, sannan ya ci gaba da tarihin rayuwarsa, inda ya bada labarin tarihin Musulunci na farko, sannan kuma ya ci gaba da yin bayani kan likitanci. inda marubucin ya tattaro magungunan annabci tare da likitancin kasar Girka, inda yayi bayani kan maganin cututtuka daban-daban tare da yin tsokaci kan wasu muhawarar da ake tafkawa a tsakanin kwararrun likitocin zamaninsa. A babin karshe na littafin, marubucin ya tabo batutuwa daban-daban a cikin Fikihun Musulunci, wadanda suka hada da hukunce-hukuncen ciniki da aure da saki.

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin littafan Sunna

Manazarta

gyara sashe

Albarkatun waje

gyara sashe