Yusa, wanda aka fi sani Tsaraki, Sarkin Kano ne daga Shekara ta alib 1136 zuwa shekara ta alib 1194. Ɗan Gijimasu ne da Yankuma (ko Yankuna).

Yusa (Sarki)
Rayuwa
Mutuwa 1194 (Gregorian)
Sana'a

Yusa ya hau gadon saruta a shekara ta alib 1136 bayan ƴan uwansa tagwaye Nawata and Gawata sun mutu. An kuma sanshi gina katangun Kano.

Yusa ya mutu a shekarar 1194 ɗan Naguji. ya gajeshi.

Tarihin A Tarihin Kano

gyara sashe

Da ke ƙasa akwai tarihin Nawata da Gawata daga fassarar Ingilishi na Palmerna a shekara ta alib 1908 Tarihin Kano .


Sarki na 5 shine Yusa, wanda ake kira Tsaraki. Shi ɗan Gijimasu ne.

Shi ne ya kammala ganuwar Kano, kamar yadda aka sani. Ya kai wa Karaie hari, ya yi sansani a Badari tsawon watanni 5 har mazauna garin sun yi masa biyayya. Daga Gurmai zuwa Farinrua mutane sun ba shi haraji. Sannan ya koma kasarsa.

Manyan mayaƙansa sune Tuje, Fasau, Iyagari, da Kamfaragi. Duk waɗannan ba su da tsoro a yaƙi.

A zamanin mulkin Yusa an fara amfani da garkuwa (Garkwa).

Ya yi shekara 60 yana sarauta. Sunan mahaifiyarsa Yankuma ko Yankuna. Ya rasu.

— Tarihin Kano

 


Last, Murray (1980). "Historical Metaphors in the Kano Chronicle". History in Africa. 7: 161–178. doi:10.2307/3171660.

Palmer, Herbert Richmond, ed. (1908), "The Kano Chronicle", Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland, 38, pp. 58–98 – via Internet Archive; in Google Books. This article incorporates text from this source, which is in the public domain.

Magabata
{{{before}}}
Sarkin Kano Magaji
{{{after}}}