Jihar Yobe tana Arewa maso gabashin Nijeriya, mafi yawan Al'ummarta manomane, an kirkireta daga jihar Borno ranar ashirin da bakwai 27 ga watan Ogusta, shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da ɗaya 1991 a lokacin mulkin janar Ibrahim Badamasi Babangida. Babban birnin jihar tana Damaturu, babbar karamar hukumar jihar kuma mafi Al'umma da kasuwanci ita ce Potiskum. Jihar tana da addinai guda biyu: Musulunci da kiristanci, duk da cewa basu dayawa.[1]

taswirar yobe
gwamnatin yobe
Mutanan kunuri

Yarukan jihar Yobe su ne;

  1. Kanuri
  2. Fulani
  3. Badewa
  4. Kare-kare
  5. Ngizim
  6. Gamo
  7. Bolewa
  8. Hausa
  9. Margi
  10. Bura
  11. Shuwa
  12. Manga.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.nigeriagalleria.com/Nigeria/States_Nigeria/Yobe/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2017-10-10. Retrieved 2023-02-28.