William Stewart Aimson (an haife shi a ranar 3 ga watan Yunin shekara ta 1994) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Ingila wanda ke buga kwallo a matsayin dan baya na kungiyar wigan Atletic.

Ayyukan Kwallonsa

gyara sashe

Aimson ya fara aikinsa a Eastleigh lokacin yana dan shekaru , Aimson ya shiga Hull City bayan ya yi kokari a gwaji da sukayk masa a can.[1] A ranar 1 ga watan Maris na shekara ta 2014, Aimson ya shiga kungiyar Firimiya ta Tamworth a kan aro. Aimson nan da nan yasamu shiga tawagar kungiyrar kuma ya fara bugawa, wasa da faduwa akan kwallaye 2-0 a kan Halifax Town.[2] Aimson yayi karin wasanni biyu ga kulob din.


Aimson ya shiga kungiyar Tranmere Rovers a kan aro a watan Nuwamba 2014 daga Hull City . [3] Ya fara buga wasan kwallon kafa a kungiyar Southend United a Prenton Park a wasan da aka yi da shi 1-2 a gasar League Two a ranar 22 ga Nuwamba 2014. [4] Aimson ya kare ka shin kafa lokacin yana wasa da Portsmouth a ranar 29 ga Nuwamba bayan haɗuwa da abokin aikinsa Danny Holmes .[5] watan Nuwamba na shekara ta 2015, Aimson ya koma kungiyar Blackpool ta League One kan yarjejeniyar aro na wata daya, [6] kodayake daga baya aka tsawaita wannan zuwa 9 ga Janairun shekara ta 2016.

cikin canjin watan Janairun 2016 an tura Aimson gaba daya zuwa kungiyar Blackpool a bisa kuɗin da ba a bayyana ba.[7] Blackpool ta saki Aimson a ƙarshen kakar 2017-18. [8] ranar 21 ga watan Yunin 2018, ya sanya hannu kan kwangilar shekaru biyu tare da kungiyar Bury, yana bin sawun kakansa Paul, wanda ya shafe shekara guda tare da kungiyar Shakers a lokacin aikinsa.[9] Aimson ya sanar da cewa ze bar kungiyar Bury a ranar 1 ga Yulin 2019, yana kiran dalilan da ya sa ya tashi "daga hannuna".

Manazarta

gyara sashe
  1. "Football: Christchurch star Will signs for Tigers". Bournemouth Echo. 29 August 2012. Retrieved 29 December 2014.
  2. "FC Halifax Town 2 – 0 Tamworth". BBC Sport. 1 March 2014. Retrieved 29 December 2014.
  3. "Tranmere sign Hull's Calaum Jahraldo-Martin & Will Aimson". BBC Sport. 20 November 2014. Retrieved 29 November 2014.
  4. "Tranmere Rovers 1–2 Southend United". BBC Sport. 22 November 2014. Retrieved 29 November 2014.
  5. "Tranmere Rovers: Hull City loanee Will Aimson suffers broken leg". BBC Sport. 2 December 2014. Retrieved 2 December 2014.
  6. "Blackpool sign Hull defender Aimson". BBC Sport. 9 November 2015. Retrieved 9 November 2015.
  7. "Defender Swaps Hull for Blackpool". Blackpool F.C. 14 January 2016. Retrieved 14 January 2016.
  8. "Manager Confirms Retained List". Blackpool F.C. 4 May 2018. Retrieved 11 May 2018.
  9. "Aimson becomes a Shaker". Bury F.C. 21 June 2018. Archived from the original on 28 January 2022. Retrieved 21 June 2018.