Wikipedia:Mahangar da ba son rai
(an turo daga Wikipedia:Rubutu a mahangar da ba son rai)
Dukkan muƙalolin insakulofidiya dake a cikin Wikipedia ya zama tilas a rubuta su daga mahangar gaskiya da adalci, mahangar da ba son rai ko kuma fifita wani al'amari saboda wani dalili. Dole ne a ba kowane al'amari hakkinsa kamar yadda yake a sahihan hanyoyin samun bayanai, ba tare da dasashe wata mahangar ko kuma fifita wata ba.
Rubutu daga mahangar da ba son rai, yana daga cikin muhimman ginshikan Wikipedia