When the Trees Fall (fim)
Lokacin da Bishiyoyi Fadi (When the Tress Fall) wani fim ne na kasar Ukraine wanda Marysia Nikitiuk bada umurni. An lissafo shi a matsayin daya daga cikin fina-finai kasar Ukraine na zamani na musamman.
When the Trees Fall (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2018 |
Asalin harshe | Harshan Ukraniya |
Ƙasar asali | Ukraniya, Poland da Masadoiniya ta Arewa |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
Launi | color (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Marysia Nikitiuk |
Marubin wasannin kwaykwayo | Marysia Nikitiuk |
External links | |
Specialized websites
|
Labari
gyara sasheAn shirya shi a wani dan karamin birnin Ukraine, Lozova, shirin ya ta'allaka ne akan wata yarinya mai shekaru biyar, Vitka, da kuma 'yar uwarta, Larysa, wacce ke soyayya da wani dan ta'adda.[1] Labarin wata yarinya 'yar tawaye Vitka mai shekaru biyar tare da 'yar uwanta Larysa da saurayinta, matashin mai laifi mai suna Scar ya bayyana a wani yanki na Ukraine. Larysa ta sami kanta a wani yanayi bayan mutuwar mahaifinta. Suna son zama tare amma al'ummar ƙauyen sun kore ta saboda tana soyayya da Scar. Larysa ta gano kakarta ta taba sadaukar da soyayyarta ga wani matashi dan gypsy ta bar shi saboda dalilai na al'ada da kuma ra'ayoyin sauran mutane. Mahaifiyar Larysa ba ta da ƙarfi da zata iya taimaka wa ’yarta. Larysa da Scar suna shirin tserewa daga rayuwar ta'addanci, wahala da kuma 'yan uwansu. Sannan a shirye suke da su fuskanci duk wani matsala saboda 'yancinssu?
'Yan wasan kwaikwayo
gyara sashe- Anastasiya Pustovit a matsayin Larysa
- Sofia Halaimov a matsayin Vitka
- Maksym Samchyk as Scar
Shiryawa
gyara sasheAn shirya fim ɗin ne bayan Nikitiuk ya lashe lambar yabo ta Krzysztof Kieslowski Script Award a matsayin mafi kyawun shiri da aka rubuta a Tsakiya da Gabashin Turai a bikin Fim na Cannes a watan Mayu 2016. Kyautar ta kasance tare da tallafin samarwa € 10,000.[2] Labarinta da ya lashe lambon yabi shine When the Trees Fall.[2][3]
An dauki shirin na When the Trees Fall ne a Ukraine da Poland.[4]
Saki
gyara sasheShirin ya fara fitowa ne a wajen bikin Berlin International Film Festival na 68 a shekara ta 2018.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Abenia, Enrique (10 December 2021). "ArteKino 2021: La sorprendente personalidad de Marysia Nikitiuk en la ucraniana 'When the Trees Fall'". Cinemanía (in Spanish). Archived from the original on 8 September 2022. Retrieved 8 September 2022.
- ↑ 2.0 2.1 "Antonenko, Alisa (19 May 2016). "Marysia Nikitiuk received a French award". The Day. Archived from the original on 8 September 2022. Retrieved 8 September 2022.
- ↑ "Marysia Nikitiuk: Today's Character is a Bad Man with a Kind Heart and an Incredible Sense of Guilt". Ukrayinska Pravda. Archived from the original on 8 September 2022. Retrieved 8 September 2022.
- ↑ Її протест - реакція людини, яка не хоче померти в цьому болоті" - кінокритик про фільм "Коли падають дерева". Gazeta.ua (in Ukrainian). 2018-02-26. Archived from the original on 14 April 2022. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ На Берлінале показали фільм української режисерки". Gazeta.ua (in Ukrainian). 2018-02-21. Archived from the original on 19 February 2022. Retrieved 2022-09-11.