Usman Bala Zango (an haifeshi a ranar 3, ga Janairun, 1963). Ya kasance ƙani ne ga Alh. Sani Zangon-Daura. Rt. Hon Usman Bala, ɗan kasuwa ne kuma gogaggen ɗan-siyasa. Shine Kakakin Majalisa na farko a Jihar Katsina.[ana buƙatar hujja] Ya riƙe mukamai daban-daban a kamfanoni mabanbanta. Shine shugaban daya kwamitin amintattu na Maryam Endowment Fund.

Farkon Rayuwa.

gyara sashe

Ya fara karatun sa na firamare a Zango One Primary School daga shekarar 1972, zuwa 1978. Daga nan ya zarce Government Secondary School Bauci daga shekarar 1978, zuwa 1981. Ya anshi kwalin WASCE a Government Secondary Funtua 1981, zuwa 1983. Ya kuma halarci Kaduna Polytechnic daga shekarar 1983, zuwa 1986, in da ya anshi shedar kamala National Diploma a fagen Business Administration.

Mukami da aiki.

gyara sashe
  • Ya rike Mukamin accounter a Hukumar Lafiya ta Jihar Katsina shekara ta 1988, zuwa 1991.
  • Shine Kakakin Majalisa na farko na Jihar Katsina daga 22, ga Janairu, 1992, zuwa 17 ga Nuwamba, 1993.
  • Commercial Manager Nation House Press Fabarairu, 1994 ,zuwa Disamba, 1995.
  • Adminin and Personal Manager Kaduna Aluminium Extrusion Ltd Oktoba, 1998, zuwa Oktoba 2002.
  • Kaduna Machine Works and Kaduna Aluminium Oktoba, 1998, zuwa Oktoba 2002.
  • Maibada Shawara na Musamman akan Harkokin Siyaya ga Gwamnan Jihar Katsina  Maryam Aminu Bello Masari Ogusta, 2015, zuwa 29, ga Mayu, 2019.
  • Shugaban Gudanarwa Maikano Digital Printing and General Services Ltd. 17, ga Yuni, 2019, har zuwa yau.
  • Shugaban Board of Trustee na Maryam Endowment Fund, 2012, zuwa yau.

Manazarta.

gyara sashe