William James Mallon (an haife shi ranar 2 ga watan Fabrairu, 1952) likitan Amurka ne, kuma tsohon ƙwararren ɗan wasan golf kuma mai jagoran wasannin Olympics.

Rayuwar farko da Fara Aiki gyara sashe

An haifi Mallon a Paterson, New Jersey. Ya yi karatu a Jami'ar Duke kuma ya kammala karatun (magna cum laude) da sakamakon A.B. a fannin lissafi da physics. Yayin da yake Duke ya buga wasan golf na kwaleji kuma ya kasance All-American sau biyu, haka-zalika sau biyu ya na zaɓar fitattun 'yan wasan Kwaleji na Amurka kuma ya kasance ɗan takara sau biyu a gasar NCAA. Ya lashe gasa sama da 40 na wasan masu tasowa (amateur) da suka haɗa da; ƙwara biyu kowanne a gasarMassachusetts Amateur da New England Amateur. [1] Har ila yau, ya lashe Middle Atlantic Amateur sau ɗaya. [1]

A matsayin ƙwararre gyara sashe

A shekara ta 1975, Mallon ya zama ƙwararre. [1] Ya shiga PGA Tour bayan ya cancanci shiga Fall 1975 PGA Tour Qualifying School. Mallon ya buga wasannin tsawon kaka huɗu, daga 1976 zuwa 1979, an zabi mafi kayatarwa uku acikin 10 na wasanni da ya kammala. Wasansa mafi kyayatarwa shi ne na 5 a 1977 Joe Garagiola-Tucson Open. Mallon ya taka leda a 1977 U.S. Open kuma ya kasance sau biyu a cikin mutane 100 a jerin masu kudin gasar.

Aikin likita gyara sashe

Bayan barin PGA Tour, Mallon ya koma Jami'ar Duke don karantar karatun likitanci a matsayin M.D. a 1984. Ya zauna a cibiyar kula da lafiya ta Jami'ar Duke tsakanin 1984 zuwa 1990 kuma yanzu shine Mataimakin Farfesa na Orthopedics kuma yana da nasa aikin na kashin kai. Mallon ya ƙware a ɓangaren haɗa/gyaran ko tiyatar kafaɗa da tiyatar gwiwar hannu kuma shi mabiyin ƙungiyar Cibiyar Nazarin Orthopedic Surgeons na Amurka, ne Hakazalika , memba na Likitan Jiki na Amurka da Jikin gwiwar hannu, inda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban wurin a shekarar 2012, kuma zai zama shugaba wurin a 2014, kuma memba. na majalisar shawara na Cibiyar Kula da Magungunan Wasanni. Ya yi rubuce-rubuce sosai kan batun raunin wasanni kuma ya kasance editan likita na Golf Digest tun 1987. A baya Mallon ya kasance editan Arewacin Amurka na Jaridar Shoulder and Elbow Surgery .

Masanin tarihin Olympics gyara sashe

Har ila yau Mallon shi ne babban jami'i a tarihin gasar Olympics kuma ya rubuta littattafai 24 kan wannan batu. Ya kasance abokin haɗin gwiwa kuma daga baya shugaban kungiyar masana tarihi na Olympics na kasa da kasa kuma ya kasance mai ba da shawara kan tarihi ga kwamitocin shirya wasannin Olympics na Atlanta da Sydney. Mallon ya kasance mai ba da shawara kan ƙididdiga ga kwamitin Olympics na kasa da kasa kuma an ba shi lambar yabo ta Olympics a azurfa a shekara ta 2001 saboda hidimar da ya yi ga Olympics.

Ƙananannasarori gyara sashe

  • 1972 New England Amateur
  • 1973 Massachusetts Amateur
  • 1974 Massachusetts Amateur
  • 1975 Middle Atlantic Amateur, New England Amateur [2]

Nasarori a matakin ƙwararre gyara sashe

  • 1976 Bude New England
  • 1977 Bude New England

Zaɓaɓɓun littafi gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named pga
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named neam