Umar Ibn Aliyu Babba (1881 – 1891) shine Kalifa Umaru Dan Aliyu Babba wanda shine Kalifa na hudu (4) a sokoto. Kuma jika wajen Muhammadu Bello Shehu Usman Dan Fodio. An haifeshi a Wurno a shekarar 1877. Umar Ibn Aliyu Babba ya fito daga ahalin Toronkawa (Torobe) dangin Fulani.[1]

Karatu gyara sashe

Kalifa Umar kamar sauran yayan sarki ya taso ne a gidan ilimi, al’ada ne na shugabannin addini su gina makarantu duk inda suke. Saboda haka Wurno, Salame , Chimmok da Sokoto duk garuruwa ne na karatu.

Tsaiko gyara sashe

An kuma samu tsaiko wajen hada tarihin Kalifa Umar inda kusan kowa ke boye tarihinsa. Dayawa daga cikin mutane sukan fadi cewa basu san komai a kanshi ba. Wannan harda yan uwanshi na jiki ma sun nuna cewa basu san komai akan shi ba.[1]

Sarauta gyara sashe

Rasuwar Kalifa Mu’azu, ta bada daman nada wani Kalifa kamar yadda addini ya tanada. Mutum biyar ne suka nemi Kalifanci a lokacin. Inda a cikin su Allah ya zabi Kalifa Umar ya bashi mulki. An kuma naɗa Umar Kalifa a shekarar 1881 a Sokoto. A lokacin yana da shekara ta 59 a duniya.

An kuma naɗa shine a Ranar Lahadi 9 ga watan Zulkida a masallacin Kalifa Bello.

Rasuwa gyara sashe

An ruwaito cewa Kalifa Umaru ya rasu ta sanadiyar harbi da doki ya masa a lokacin da yake shafanshi, da yammaci. Ya rasu a fadar sarkin Kiyawan Kaura Namoda a ranar Laraba 25 ga watan maris, shekarar 1891. A lokacin yana da shekara (69). Yayi mulki na tsawon shekara (9) da wata goma (10).[1]

Bibiliyo gyara sashe

  • Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN 978-978-956-924-3. OCLC 993295033.
  • The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.
  • Smaldone, Joseph P. (1977). Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. p.p 171-191 ISBN 978-978-956-924-3.