Umar Abdul'aziz fadar bege
Umar Abdul-Aziz Baba wanda akafi sani da (Fadar Bege) An haife shi a garin Garko karamar Hukumar Wudil a da, wanda a yanzu tazama Karamar Hukuma mai zaman kanta a Jihar Kano, a ranar Alhamis a shekarar alib 1974. Shi dai Umar abdul'aziz shahararren mawakine ne, na begen Annabi Muhammadu (s.a.w) a cikin harshen Hausa. Matashine maijini ajika, allah yajikanshi ameen
Tarihi
gyara sasheMahaifinsa Mal Umar, mai Unguwa ne a wani kauye dake garin Garko, bayan rasuwar mahaifin Fadar Bege lokacin yana dan shekara hudu (4) sai suka dawo Karamar Hukumar Wudil da zama shida mahaifiyarsa mai suna Malama Hadiza, kasancewar dama aikine yakai mahaifin nasa Mai Unguwa garin na Garko lokaci da take hade da karamar hukumar Wudil.
Ilimin Addini da na zamani
gyara sasheFadar Bege ya fara karatun Alonsa ne a wata makaranta mai suna MAKARANTAR MALAM YAYA, a wurin wani mashahurin Malami dake cikin Karamar Hukumar Wudil mai suna Alaramma Malam Musa Yaya, wanda a yanzu haka shine shugaban Malamai na Karamar Hukumar Wudil.
Fadar Bege ya koma cikin Birnin Kano ne a shekarar 2000, domin kara faɗaɗa iliminsa na addinin Islama, inda a nan ne ya gamu da babban shehin malamin cikin birnin Kano wato Sheikh Sharif Sani Jambulo
Fadar Bege ya fara Karatunsa na Primary a Wudil Special Primary School a shekarar alif 1981, ya kammala karatunsa na Primary a shekarar alif 1986. Sannan ya tafi Makarantar Koyan Kasuwanci dake Wudil, wato Government Secondary Commercial School Wudil a shekarar alif 1986, ya kuma kammala karatun a shekarar alif 1992.
Fadar bege bai tsaya a nan ba bayan kammala karatunsa na Sakandire, saikuma ya famtsama akan neman karatun adini iri daban daban a gurin Maluma masu tarin yawa, na ciki da wajen garin wudil, a karshe yazama shima mai bada karatu a Islamiya dake garin na wudil.
Sana`a
gyara sasheMarigayi Fadar Bege yayi sana’o’i da dama daga ciki har da wacce akasan duk wani dan wudil da yinta wato sana’ar dinkin Kwado Da Linzami,
Sannan marigayi Fadar Bege yayi sana'ar Tireda bai tsaya a iya nan ba yayi sana'ar daukar hoto.[1]
Sannan yana hadin gwiwa da mahaifiyarsa wajen sana’ar Shinkafa.
Asalin fara wakar bege
gyara sasheBayan shawarwari da akayi ta bashi na daga 'yan uwa da abokan arzuka kan ya fara wakar kansa, Allah cikin ikonsa sai ya fara yin waka mai taken SAYYADI NASOKA YA SHUGABAN ALUMMA BABU YAKAI YA SHUGABANA, a shekarar alib 1992 wacce aka kaddamar a karamar hukumar Wudil Unguwar Kofar Fada bakin Jan-bulo, wanda Wakar tasamu zuwan babban sha’iri daga cikin birnin Kano wato Alhaji Sani Mai Sa’a ya kaddamar da wakar.
Hira da amininsa
gyara sasheCikin zantawar da shafin Alummar Hausa yayi da babban amininsa dake karamar hukumar Wudil wato Komared Aminu Mamanu Wudil, ya shaidawa Alummar Hausa cewa Wakokin marigayin suna da matukar yawa don kuwa koshi kansa Marigayi Fadar Bege baisan iya adadin wakokinsa ba.
Amma daga cikin Wakokin nasa ya bayyanawa Alummar Hausa wadanda sukafi shahara a wurin mutane, wadanda suka hada da;
- Labbaika Rasulillah
- Farkon Mafadi,
- Ya Mustapha Zuljudi,
- Assalamun-Alaika,
- Aahalan Wassahalan,
- Dan Asali,
- Annabi Ni Ina Gaida Kai,
- Maula Inyass,
- Lamuni Nake Nemah,
- Mai Babban Masallaci,
- Nagaban Hankali,
- Takalminka Yafi Kowa,
- Murhun Gidan Annabi,
- Mai Cikar Asali Ne,
- Mahamudu Ma’aiki Na[2]
Rasuwa
gyara sasheFadar Bege ya rasu a shekarar 2013, sakamakon rashin lafiyar da ya kwanta a asibiti. Yabar mata da yara biyu. Allah ya jikansa da rahama yasa Aljannah tazama makoma tare da dukkan musulmai baki daya amen summa amin.[3]