Tumasanci shi ne zama a gurin wani mai kuɗi ko basarake a yi ta zance da nufin taya wannan mai kuɗin ko basaraken hira. Ba komai ake yi a irin waɗannan zantuttuka ba sai faɗin abubuwan da za su daɗaɗawa wannan mutum rai, ko da kuwa maganar za ta kai a muzanta wani wanda ake ganin, tsakinsu da tsakuwa tsakaninsa da wannan mutum.

Bayan haka kuma akan saka maganganun ban dariya, a wasu lokutan ma akan kawo labaran abubuwan da ke faruwa a gari, da sauran abubuwa makamantan wannan.

Wannan al'ada ce da aka fi samun ta a kasar Hausa.

Manazarta:

gyara sashe

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.