Tsunburbura
Tsunburbura gunki ce ko kuma aljana da Maguzawan Kano suke bauta mawa a yankin Dutsen Dala a ƙarni na goma 10th, wanda Barbushe yake jogorantan bautan, zuwan Ɗan Zubua da Usman Dan Fodiyo suka yake su, sannan suka karya bautan.[ana buƙatar hujja]
Tarihi
gyara sasheWasu mafarauta sun zauna a Dutsen Dala, Gwauron Dutse, magwan da kuma fanisau,[1] Waɗannan mutanen suna yi tsafi ne da kuma bautawa aljana ko Gunki mai suna tsunburbura, Barbushe shine babban malamin wannan bauta. Duk farkon shekaran kalandan Hijira, Barbushe yana shiga cikin wannan gidan tsafin yazo ma mutane da sabon saƙo, inda jama’a suke taruwa kewaye da gidan suna jiran saƙo, idan aka gaya musu saƙon, sai suyi yanke-yanke na akuyoyi da karnika ga Tsunburbura.[1]