Tolulope Popoola
Tolulope Popoola marubuciya ce 'yar Najeriya wacce ta ƙware a cikin rubutun Littattafan soyayya. An nuna rubuce-rubucenta da sassan labaranta a cikin wallafe-wallafe da mujallu da yawa.
Ayyuka
gyara sashePopoola ta fara rubutu a shekara ta 2008, bayan ta yi murabus daga aikin da take da kamfanin lissafi. Ta rubuta littafinta na farko a shekara ta 2009, amma ta yanke shawarar bazata wallafa ba bayan ta gano cewa ya yi kama da In Dependence na Sarah Ladipo Manyika . A shekara ta 2012, ta wallafa Littafin soyayya na farko, Nothing Comes Close . Littafin an jera shi a matsayin daya daga cikin littattafai mafi kyau na 2012 a kungiyar African Writers Club.