The Guardian (Najeriya)
The Guardian jarida ce mai zaman kanta a Najeriya, wacce aka kafa a cikin shekara ta 1983, wacce jaridar Guardian Limited ta samar a Legas, Najeriya.[1]
The Guardian | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | takardar jarida |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1983 |
|
Tarihi
gyara sasheAlex Ibru, ɗan kasuwa, da shi da Stanley Macebuh, babban ɗan jarida tare da jaridun Daily Times ne, suka kafa The Guardian a cikin shekara ta 1983. An kwafi samfurin jaridar daga ainihin jaridar The Guardian ta Burtaniya. The Guardian ta kasance majagaba wajen gabatar da aikin jarida mai inganci a Najeriya tare da ingantattun rahotanni.[2] An fara buga labaran jaridar ne, a ranar 22 ga watan Fabrairu, 1983 a matsayin wallafa labarai duk mako-mako, wato tana fitowa a duk ranar Lahadi. An fara buga labarai a kullun, a ranar 4 ga watan Yuli, 1983.[3]
A lokacin mulkin soja na gwamnatin Janar Muhammadu Buhari, an tura manema labarai da suka haɗa da; Tunde Thompson da Nduka Irabor a gidan yari a shekarar 1984 a ƙarƙashin doka mai lamba 4 ta 1984, wadda ta danne ƴancin aikin jarida.[4][5] A ranar 26 ga watan Agustan 1989 jaridar The Guardian ta buga wata doguwar wasika daga Dokta Bekolari Ransome-Kuti, mai fafutukar kare hakkin bil’adama, mai taken “Budaddiyar Wasika zuwa ga Shugaba Babangida”, inda ya soki abin da ya ke ganin na ƙara murkushe ƴancin fadin albarkacin baki da gwamnati ke yi.[6]
Yunƙurin kisa
gyara sasheMamallakin Jaridar Alex Ibru, ya tsallake rijiya da baya a yunƙurin kashe shi a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.[7] A ranar 2 ga Fabrairun 1996 aka harbi motarsa kuma aka kai wa Ibru hari. An garzaya da shi asibiti idanunsa na lumshewa. Bayan mutuwar Sani Abacha, ta ba zato ba tsammani a watan Yuni 1998, an fara shari'a akan ɗansa Mohammed Abacha da babban jami'in tsaro Major Hamza al-Mustapha . Daga karshe dai a watan Disambar 2010 wata babbar kotun Legas ta wanke waɗanda ake zargi da yunƙurin.[8][9]
The Guardian
gyara sasheKamfanin Jaridar The Guardian mallakar wani memba a ƙungiyar ethnic minority ce. Jaridar ta kasance mai mutunta ra'ayin kowace kabila, al'ummar addini, jam'iyyar siyasa ko wata kungiya mai wani ra'ayi . Sai dai ana zargin jaridar da nuna kiyayya ga kabilar Ibo.[10]
Daraja
gyara sasheJaridar New York Times ta bayyana Guardian a shekarar 1988 a matsayin "jarida mafi daraja a Najeriya".[11]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "The Guardian". JournalSeek. Archived from the original on 16 July 2011. Retrieved 14 May 2011.
- ↑ Linda K. Fuller (2004). National Days/National Ways: Historical, Political, and Religious Celebrations Around the World. Greenwood Publishing Group. p. 171. ISBN 0-275-97270-4.
- ↑ "With The Guardian, Alex Ibru came, saw and conquered". The Guardian (in Turanci). 2018-07-04. Archived from the original on 2022-05-23. Retrieved 2022-05-23.
- ↑ Stanley Mokaogwu (19 March 2011). "Investigative Journalism: A Panacea For Corruption". Nigerian Observer. Archived from the original on 24 March 2011. Retrieved 14 May 2011.
- ↑ Omomia, Kassim (20 April 2011). "Buhari And The Subtle, "No Court Declaration"". Nigerian Pilot. Archived from the original on 23 August 2011. Retrieved 14 May 2011.
- ↑ Johnson-Odim, Cheryl; Mba, Nina Emma (1997). For Women and the Nation: Funmilayo Ransome-Kuti of Nigeria. University of Illinois Press. p. 177. ISBN 0-252-06613-8.
- ↑ Khena-Ogbena, Clem (9 January 2011). "How Al-Mustapha, Others Were Cleared". Leadership. Retrieved 14 May 2011.[permanent dead link]
- ↑ Sanda, Julcit (26 February 2003). "Ibru: Mohammed Abacha Heads for Appeal Court". ThisDay. Retrieved 14 May 2011 – via All Africa.
- ↑ Dada, Paul (22 December 2010). "Attempted Murder of Alex Ibru – Al-Mustapha, Others Cleared". Leadership (Abuja). Retrieved 14 May 2011 – via AllAfrica.
- ↑ Siapera, Eugenia (2004). At the Interface: Continuity and Transformation in Culture and Politics. Rodopi. pp. 68ff. ISBN 90-420-1732-5.
- ↑ "Lagos Journal; A Gleeful David Faces the Goliath That Is Nigeria". The New York Times. 28 October 1988. Retrieved 14 May 2011.