Tebelelo Mazile Seretse ita ce mace ta farko da ta zama jakadiyar Amurka daga Botswana (wacce ta fara aiki a ranar 14 ga watan Fabrairu, 2011). Yayin da ta kasance 'yar majalisa daga shekarun 1999 - 2004, tana da muƙaman majalisar ministoci uku: Mukaddashiyar Ministar Harkokin Shugaban Ƙasa, Ministar Kasuwanci da Masana'antu, Dabbobin daji da Yawon buɗe ido da Ministar Ayyuka, Sufuri da Sadarwa.[1]

Ta kasance Darakta kuma Shugabar RPC Data Limited, "kamfanin sabis na fasahar sadarwa mafi girma a Botswana." [2]

Seretse ta kammala karatu daga Jami'ar Jihar Morgan da BA a fannin tattalin arziki da BA a fannin Accounting kafin ta sami MA a Jami'ar Cincinnati da LL. B. digiri na shari'a daga Jami'ar Botswana.[1]

A watan Satumba na 2021, Ministan Ilimi, Bincike, Kimiyya da Fasaha (MoTE), Dokta Douglas Letsholathebe, ya sanar da naɗin Ambasada Tebelelo Mazile Seretse a matsayin Shugabar Jami'ar Botswana. Shugaba Mokgweetsi Masisi ne ya yi naɗin kuma ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba 2021 har zuwa ranar 31 ga watan Agusta 2026.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Tebelelo Mazile Seretse". Meridian International Center. Retrieved 13 July 2020.
  2. "TEBELELO MAZILE SERETSE". World Affairs Council. Archived from the original on 26 October 2022. Retrieved 13 July 2020.