Tattaunawa:Abdullahi aliyu alkas

LABARI MAI BAN TAUSAYI LABARIN ALHAJI KABIRU TANIMU MAI TAYAR DA HANKALI Daga:-Yasir Ramadan Gwale 03-08-2013 Alhaji Kabiru Tanimu, mutum ne da Allah ya yiwa arziki, ya mallaki abin duniya fiye da duk yadda mai misali ya kai da iya misaltawa. Alhaji Kabiru Tanimu, yana kasuwancin Gahawa, Citta, Kanimfari, Masoro, Tafarnuwa, Ganyen-Shayi da zobo-rodo a kasashen Kenya, Afurka-Ta-Tsakiya, Nijar, Tchadi, Sudan, Indiya, Chana, Singarore, Malaysiya da kuma kasashen Turai da Amerika, Alhaji Kabiru Tanimu, yana da manyan gonakin Noma wadannan kayan da yake kasuwancinsu a kasashe da dama, haka kuma, yana da manyan dakunan adana wadannan kaya a Najeriya da Nijar da sauran kasashe da dama, sannan kuma yana da kamfanunuwa na sarrafa su a Chana da Singapore da Indiya da kuma Najeriya, wannan ta sanya Alhaji ba shi da wani lokacin kansa, shi yasa kullum yana kan hanya daga wannan kasa zuwa waccan kasa. Allah cikin kudurarsa ya sanyawa Alhaji Kabiru Tanimu zuciyar taimako. Yana da san taimakawa masu karamin karfi da gajiyayyu da masu bukata, yana kyauta baya gajiyawa, kullum hannunsa a bude yake, duk wad’an da suka san Alhaji sun shaideshi akan haka; sannan kuma mutum ne mai kula da Sallah, baya sake da lokacin Sallah a duk inda yake, haka idan lokacin Azumi ya zo gidan Alhaji kan cika makil da mutane daga masu karbar buhun-hunan kayan abinci zuwa masu karbar kudi da kayan sawa da dai sauransu. Alhaji Kabiru Tanimu, yana da matan aure guda uku, dukkanninsu suna zaune a kasashe daban-daban, domin matarsa ta farko tana birnin Kano a Najeriya, ta biyu na Saudi Arebiya ta ukun kuma na kasar Malaysiya. Saboda irin yanayin kasuwancin Alhaji ya sa, sai ya shafe tsawon watanni hudu zuwa biyar bai tako Najeriya ba, gidansa kuwa babu wani abun bukata da iyalansa suke nema da yake yankewa, ga motoci na Alfarma ga dukkan abubuwan bukata na rayuwa, ‘yan aiki kuwa kowanne yana yin hidimar gabansa, tun daga masu share gida, wankin mota, ban ruwan fulawa, masu gadi da sauransu. Hajiya Samira itace matar Alhaji ta farko, sun shafe kusan shekaru goma sha biyar da Aure, amma d’a d’aya Allah ya albarkace su da shi mai suna Faisal dan shekaru takwas, wannan yaron na Alhaji shine babban dansa yana samun kulawa ta musamman daga wajen Alhaji yana matukar ji dashi, ana kula da karatunsa da dukkan bukatun rayuwarsa, yaro ne dan lukurkuti daga ka ganshi kasan ya sha madara babu wata alamar wahala ko gajiya a tare da shi; shima Faisal duk da kasancewarsa Yaro ya dauko halin mahaifinsa wajen sakin fuska da wasa da dariya da san yin mu’amala da sauran yara, domin Faisal ko abinci baya yarda ya ci shi kadai sai ya gayyato sauran yara abokansa, suci su sha su yi kokaye-kokayensa na kuruci dangin hauka. Wani babban tashin hankali da Hajiya Samira matar Alhaji Kabiru Tanimu take ciki shi ne na rashin samun sukuni tare da mijinta wajen debe mata kewa, da kuma samun sukunin aure tsakaninsu, ko shakka babu wannan al’amari yana matukar damun Samira, domin zata ci dukkan irin nau’I na kayan dad’i da abinsha dole ne kuma idan wadannan abubuwa suka samu ta bukaci wanda zai dauke mata bukatuwa irin na ma’aurata. Wannan ta sanya Hajiya Samira ta kasa jurewa rashin Alhaji a lokacin da ta bukace shi, inda ta fara kokarin shawo kan Hamza Muhammad daya daga cikin manyan yaran Alhaji. Hakika Alhaji ya aminta da Hamza kamar dansa na cikinsa, domin Hamza yasan sirrikan Alhaji sosai wani zubinma ita kanta Hajiya Samira a wajensa take samun labarin wasu al’amuran na mijin nata, domin babu daya daga cikin kasashen da Alhaji yake zuwa face sun je da Hamza. Hajiya Samira ta ringa nunawa Hamza irin bukatunta a gareshi, tun baya ganewa har yazo ya fara fahimtar halin da ake ciki. Daga lokacin da Hamza ya fahimci halin da Hajiya ta shiga na tsananin bukatarsa, hankalinsa ya yi matukar tashi, domin babban abinda yake tunani shi ne dangantakarsu da Alhaji Kabiru Tanimu, tayaya mutumin da ya daukeshi tamkar d’an da ya Haifa, amma ya ci Amanarsa. Ana cikin tsaka da wannan mawuyacin hali da Samira da Hamza suka shiga ne sai shi Hamza ya lura da wasu kawayen Hajiya Samira da suke yawan zuwa gidanta a kullum musamman da daddare cikin mummunar shiga, ganin wadannan mata hankalinsa ya kara tashi, domin bai gamsu da yawan zuwa da suke wajen Samira ba, da ya matsa bincike akansu aka tabbatar masa da cewar wadannan mata mafiya yawancinsu ‘yan Neman mata ne! Jin wannan labari ya sa Hamza ya fashe da kuka hankalinsa yayi matukar tashi, domin kuwa yasan rayuwar Hajiya zata shiga wani irin mummunan gararin da Allah ne kadai ya san irinsa. Hamza yana tunanin ga Samira na kawo masa hari, yana kaucewa tare da mayar da kansa bagidaje duk dan ya nuna mata shi bai fahimci abinda take nufi ba, sannan kuma a gefe guda ga wasu kartin mata suna kawowa Hajiya Samira hari babu dare babu rana! Wannan abin ya dugunzuma Hamza ainun. Bincikensa ya nuna masa cewa ita Hajiya bata san manufar wadannan kawayen da suke zuwa wajenta ba. Daga nan shima Hamza ya shiga wata tsaka mai wuya ta gaba kura baya siyaki, domin yana tunanin shin ya yi watsi da bukatun Hajiya ya kyaleta ta fada hannun wadancan batagarin mata, ko kuwa ya kare ta daga fadawa waccan halaka, ta hanyar cin amanar mai-gidansa Alhaji Kabiru Tanimu! Wannan al’amari ya tayar da hankalin Hamza matuqa, babban abinda yake damunsa shine Alhaji mutum ne da babu wanda zai zargeshi da cewa d’an duniya ne, a bisa abin da ya bayyana na zahiri dangane da rayuwar Alhaji Kabiru Tanimu mutumin kirki ne, ana kyautata masa zato, amma kuma ga irin halin da ya jefa iyalinsa a ciki. Hamza yace ina matkar jin tausayin Alhaji Kabiru Tanimu, domin shakka babu Allah ya yi masa arziki mai tarin yawa, amma ni Hamza banga alamun cewa Alhaji yana jin dadin dukiyarsa ba, a cewar Hamza, domin suturar da yake sanyawa ba wata mai tsada bace, haka duk da irin jibga-jibgan motocin da suke cikin gidajensa a Ahmadu Bello Way, da GRA Tarauni da NNDC Quarters da Tal’udu a Kano amma sai ka samu motar da Alhaji ke hawa daga Akori-kura Hillux, sai wata karamar Tayota Karina, idan kaga Alhaji ya hau daya daga cikin manyan Marsandinsa to ko dai zaije daurin aure ne, ko kuma zaije Abuja ko Kaduna, sannan gashi duk sadda yake gida abincinsa daga Tuwan Gero miyar kuka sai kunun tsamiya, shine cin dafaffiyar gyada da gujjiya da zogale da rama, wadannan da wasu abubuwa da nake gani ya sa nake tunanin anya Alhaji yana jin dadin wannan dukiya tasa kuwa? Hamza yana tattauna irin wadannan abubuwa a cikin ransa. Wani Karin abin mamaki dangane da Alhaji, idan yana Najeriya jama’a basa barinsa ya sake kullum mutane ne ke zuwa wajensa shi kuma baya korafi, kuma baya korar mutane, indai ka samu ganin Alhaji tabbaci hakika ba zaka fito daga falonsa hannu rabbana ba; mutanan da Alhaji ke daukar dawainiyar ratyuwarsu suna da yawan gaske, yara da mata da matasa da dalibai masu karatu a jami’a, bugu da kari Alhaji mutum ne mai tsananin son yara kanana, domin a yanzu haka a cikin gidan Alhaji ba zaka rasa kekunan yara sama da guda hamsin ba wadan da yake saya kawai dan rabawa yara kanana, da sauran kayayyakin wasanni na yara; Faisal dan Alhaji kuwa duk sadda Alhaji ke gari to tare zaka gansu duk inda Alhaji zai je tare suke tafiya. Ire-iren wannan rayuwa ta Alhaji Kabiru Tanimu ya sanya Hamza ke tausaya masa, sannan kuma yake ganin tayaya zaici Amanar wannan bawan Allah, a gefe guda kuma itama Hajiya Samira ta shiga cikin wani irin mawuyacin Hali, nan Hamza yake ta neman Mafita shin ya bayar da kai bori ya hau a wajen Hajiya dan kare ta daga wadancan fandararrun mata masu kawo mata farmaki, ko kuwa ya kyaleta komai ta fanjama fanjam, wannan tunanin ya sanya Hamza zubar da hawaye.

Fara tattaunawa akan Abdullahi aliyu alkas

Fara tattaunawa
Ku dawo shafin Abdullahi aliyu alkas.