Taska Daga Cikin Taskokin Aljannah

TASKA DAGA CIKIN TASKOKIN ALJANNAH

Daga Abu Musa Al-Ash'ary (Allah Ya ƙara masa yarda), ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce da ni:

"Shin ba na nusar da kai wata taska daga cikin taskokin Aljannah ba? Sai na ce: ƙwarai ka nusar da ni, sai Annabi ya ce ita ce: LAA HAWLA WA LAA ƘUWWATA ILLAA BILLAAH - ma'ana - (Babu wata dabara kuma babu wani ƙarfi sai ga Allah)"

_Imamul Bukhari da Muslim_